Hukumar Tara Haraji ta jihar Kebbi ta bayyana cewa kashi 70% na motoci da babura da ake hawa a jihar ba su da rajista.
Shugaban hukumar Illyasu Arzika-Jega ya sanar da haka da yake hira da manema labarai a ofishinsa dake Birnin- Kebbi kan matakan da gwamnati ta dauka domin kawo karshen rashin yi wa ababen hawa rajista a jihar da mutane ke yi.
Hukumar Tara Haraji na jihar ta hada hannu da jami’an tsaro a jihar domin ganin mutane sun yi wa ababen hawan su rajista a jihar.
“Idan muka kama babur ko motan da basu da rajista dole sai mutum ya yi rajista kafin mu saki motar ko babur din da muka kama.
” Muna da isassun lambobi ababen hawa da mutane za su iya siya a duka kananan hukumomin dake jihar.
Arzika-Jega ya ce gwamnati ta dauki wannan mataki ne saboda yadda ofishinsu ke yawan samun rahotanin sace-sacen motocin a jihar da yadda jami’an tsaro ke kiran ofishin su daga jihar Legas domin tabbatar da ingancin lambobi da rajistan motocin da suka kama.
Ya ce yi wa mota ko babur rajista hanya ce dake taimakawa wajen gano mota ko babur din da aka sace.
Sannan haka na taimakawa wajen samar wa gwamnati kudaden da za ta samar wa mutane ababen more rayuwa.