Kwamishinan tsaron jihar Kaduna Samuel Aruwan ya bayyana cewa ‘yan bindiga sun kashe mutum 9 sannan sun ji wa biyu sun ji rauni a kananan hukumomin Chikun, Zaria, Igabi da Zangon Kataf.
Aruwan ya kara da cewa gwamnati ta samu labarin haka ne daga bayanan da jami’an tsaro dake aiki a jihar suke sanar mata.
Aruwan ya ce ‘yan bindiga sun kashe mutum uku a kauyen Buruku-Udawa a dalilin rufe hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari da suka yi a karamar hukumar Chikun.
“Maharan sun kashe Umma Ibro-Kontagora, Abdullahi Noma-Kontagora da wani da ba a san sunan sa ba sannan Jamilu Kafinta Udawa ya samu raunin harsashi a jikinsa kuma yana kwance a asibiti.
“A kauyen Yola-Kadi ‘yan bindiga sun kashe Danjuma Maiungwa, mutum daya ya ji rauni.
A kauyen Sako dake karamar hukumar Zangon Kataf ‘yan bindiga sun kashe Samson Maza da David Garba.
“Jami’an tsaro sun tsinci gawar mutum biyu a kauyen Kurfi-Magamiya inda bayan bincike aka gano cewa gawarwakin Nehemiah Abba da Samuel Gwazah ne.
A karamar hukumar Zaria ‘yan bindiga sun kashe Alhaji Habibu a kauyen Saye.
Kwamishina Aruwan ya yi alhinin rasuwar wadanda aka kashe sannan ya ce gwamnati za ta ci gaba da samarwa mutanen jihar tsaro duk da matsalolin da ake samu.
Discussion about this post