Kwamishinan tsaron jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya sanar cewa jami’sn tsaro sun sanar da gwamnatin Jihar ranar Lahadi cewa ƴan bindiga sun dira kauyukan Kauran Fawa, Marke, Riheya dake karamar hukumar Giwa, inda suka yi kan mai uwa dawabi da ruwan harsashi har suka kashe mutum 20.
Daily Nigerian ta ruwaito cewa Aruwan ya ce rahoton da aka mika wa gwamnati ya suna cewa bayan kisan mutum 20 da ƴan bindiga suka yi sun babbake motocin mutane da babbar motar daukan kaya.
Bayan haka sun babbake rumbunan kayan gona a kauyukan sannan suka arce cikin daji.
Aruwan ya ce gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai yayi alhinin rasuwar waɗanda suka rasu, sannan ya umurci hukumar agajin gaggawa ta jihar ta gaggauta kai wa mutanen kauyun agaji.
Sunayen waɗanda aka kashe sun haɗa da:
1. Rabi`u Wada
2. Salisu Boka
3. Alh Nura Nuhu
4. Alh Bashari Sabiu
5 Alh Lawal Dahiru
6. Abbas Saidu
7 Inusa Kano
8 Malam Lawal Nagargari
9. Malam Aminu
10. Lawal Maigyad
11. Alh Mustapha
12 Lawal Aliyu
13 Sale Makeri
14 Sani Lawal
15 Auwal Umar
16 Jamilu Hassan
17 Badamasi Mukhtar
18 Malam Jibril
19 Lawal Tsawa
20 Sule Hamisu
21 Sadi Bala
22 Kabiru Gesha
23 Abubakar Sanusi
24 Saiph Alh Abdu
25 Haruna Musa
26 Lawal Hudu
27 Malam Shuaibu Habibu
28 Malam Yahaya Habibu
29 Abubakar Yusuf