Duk da halin ƙaƙa-ni-ka-yin da ‘yan Najeriya ke ciki na ƙuncin rayuka da rashin tsaro, Ministar Harkokin Kuɗaɗe Zainab Ahmed ta bayyana cewa akwai yiwuwar gwamnatin tarayya ta fito da sabbin hanyoyin karɓar haraji cikin shekarar 2022, mai kamawa nan da bayan makonni biyu.
Zainab ta ce akwai buƙatar ƙarin samun kuɗaɗen haraji domin ƙara wa daɓe makuba, tunda a cewar ta, “yanzu tattalin arzikin Najeriya ya hau miƙaƙƙar hanya da babu karkata ko waskiya.”
Zainab ta fitar da wannan furuci a lokacin da ta ke wa masu ruwa da tsaki jawabi wurin sauraren Kudirin Dokar Kuɗaɗe ta 2021, taron da Kwamitin Majalisar Tarayya kan Harkokin Kuɗaɗe ya shirya a ranar Litinin, a Abuja.
Ta ce a cikin ƙudirin an gabatar da shawarwarin gyare-gyare, inda ta ce kuma wasu harajin ma za a ƙara fito da su a cikin tsakiyar shekarar 2022 ɗin.
“Mu na nan mu na shirin bijiro da sabbin ƙudirori a tsakiyar 2022.” Inji Zainab.
Sai dai kuma ta ce Ma’aikatar Harkokin Kuɗaɗe ta kauda kai daga yin magana kan Harajin ‘VAT’ da na ‘La’ada Waje’, saboda batutuwan su na kotu, saboda wasu sun shigar da gwamnatin tarayya ƙara a kan harajin biyu.
Idan ba a manta ba, Jihar Ribas ta yi nasara a Kotun Tarayya cewa ita ke da alhakin karɓar harajin VAT ba tarayya ba, lamarin da Gwamnatin Tarayya ta ɗaukaka ƙara.
Jiki Magayi: Tulin Hanyoyin Harajin Da Za A Bijiro Cikin 2022:
“Tuni mun tsara ƙudiri da daftarin yi wa dokokin kuɗaɗe kwaskwarima domin ƙara danƙara haraji a ƙasar nan. Musamman a ɓangaren harajin cikin gida, tsarin tasarifin kuɗaɗen harajin, sai kuma harajin da ake karɓa daga kayayyakin da ake shigowa da su daga waje, sai harajin gyaran tsarin karɓar harajin da kuma tsarin yadda gwamnati ke sarrafa kuɗaɗen harajin.
“Akwai daftarin gyaran Dokar Masu Manyan Hannayen Jari, Dokar Harajin Kuɗaɗen Shigar Kamfanoni, Dokar Kafa Hukumar Tara Haraji ta Tarayya (FIRS), Dokar Harajin Kuɗaɗen Shigar Ɗaiɗaikun Mutane, Dokar Harajin La’ada Waje, Dokar Harajin Jiki Magayi da sauran su.
Discussion about this post