Hukumar Sa-ido Kan Masu Karkatar Da Kuɗaɗe Ta Haramtacciyar Hanya (NFIU), ta ƙaryata wani rahoto da Ƙungiyar ECOWAS ta fitar cewa a kowace shekara ‘yan ta’addar ISWAP/Boko Haram na karkatar da naira biliyan 18 daga Najeriya.
NFIU, wadda a Turance ake kira ‘Nigerian Financial Intelligence Unit, ta ce rahoton kwata-kwata ba gaskiya ba ne, ƙarya ce.
Sashen Bin Diggigin Kuɗaɗe na ECOWAS da ake kira GIABA ne ya fitar da rahoton, inda ya ce ISWAP na tara kuɗaɗen ne daga hada-hada da ɗan karen harajin da su ke karɓa daga hannun jama’a a Yankin Tafkin Chadi, kuma a bisa tsarin tasarifin kuɗaɗe na Najeriya, a duk shekara.
To amma kuma wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun Kakakin Yaɗa Labarai na NFIU, Ahmed Dikko, ya ƙaryata wannan rahoto, ya na mai cewa ƙage ne, kuma ƙirƙirarre ne.
ECOWAS ta ƙirƙiro GIABA cikin 2000, domin lura, sa-ido da daƙile safarar kuɗaɗen haram a cikin ƙasashen Afrika ta Yamma.
Rahoton dai ya nuna cewa ISWAP na tara kuɗaɗen shiga aƙalla dala miliyan 36 (kwatankwacin naira biliyan 18) a duk shekara, domin ta fi ƙarfin Boko Haram.
Rahoton ya ci gaba da cewa mafi yawan kuɗaɗen na fitowa ne daga harajin da ƙungiyar ‘yan ta’addar ke ƙaƙabawa ga masu hada-hadar kasuwanci a Yankin Tafkin Chadi, cikin Najeriya.
Sai dai kuma NFIU ta ce “rahoton ai kwantai ne, tun wani tsohon rahoto ne da aka taɓa fitarwa cikin 2919, wanda ba shi da wani tasiri a yanzu.”
Hukumar ta ce tuni hukumomin daƙile ayyukan safarar kuɗaɗen ‘yan ta’adda su ka daƙile wannan ɓarnar.
Lamarin dai ya zo ne daidai lokacin da Dubai ta bayyana sunayen wasu mutane shida ‘yan Najeriya da ta ce su na cikin jerin sunayen ‘yan ta’adda. Shekara ɗaya kenan bayan ƙasar ta ɗaure wasu ‘yan Najeriya da aka kama da laifin ɗaukar nauyin Boko Haram.
Discussion about this post