Hukumar Zaɓe ta Ƙasa ta buƙaci ta gabatar da kasafin naira biliyan 305 ga Majalisar Tarayya, domin yin zaɓen 2023 da kuɗaɗen.
Shugaban INEC Mahmood Yakubu ne ya gabatar da kasafin ga Kwamitin Kasafin Kuɗi na Majalisar Dattawa, a ranar Litinin.
Kwamitin ya gayyaci INEC cewa INEC ta sanya kasafin kuɗaɗen da za ta kashe wajen zaɓen 2023 a cikin kasafin kuɗaɗen ta na 2022, domin Majalisar Dattawa da ta Tarayya sun yi nazarin kuɗaɗen kuma su amince.
A ranar Talata ce ake sa ran majalisun biyu za su rattaba amincewar su da adadin kuɗaɗen da za a kashe a lokacin zaɓen.
Naira Biliyan 305 Ɗin Daban Su Ke Da Naira Biliyan 40 Kuɗin Kasafin Shekara:
Farfesa Yakubu ya bayyana cewa waɗannan naira biliyan 305 da hukumar ke nema, daban su ke da naira biliyan ɗin da INEC ɗin za ta kashe wajen ayyukan ofishin ta na cikin kasafin 2022.
Yakubu ya ce an rigaya an damƙa wa INEC naira biliyan 100 domin fara shirye-shirye, waɗanda shugaban na INEC ya ce adadin sun yi kaɗan a fara shirye-shiryen zaɓen 2023 da su.
“Mun damƙa masu kasafin naira biliyan 305 domin aikin zaɓen 2023 da su.
Bayanan kasafin dai ya ƙunshi shafuka 22. Waɗancan naira biliyan 40 kuwa, kuɗaɗen ayyukan yau-da-kullum ne na ofishin INEC, ciki har da gudanar da zaɓukan da a kan gudanar ba lokacin ɗaya da babban zaɓe na ƙasa ba.
“Ya kamata wannan kwamiti ya sani cewa nan gaba akwai zaɓukan cike-gurabu har guda takwas, guda uku zaɓen ɗan majalisar tarayya ne, sauran biyar kuma na majalisar dokoki ta jihohi ne.
Shugaban Kwamitin Kasafin Kuɗaɗe, Sanata Barau Jibrin, ya ce za a saka kuɗaɗen gudanar da zaɓen 2023 a cikin kasafin 2022.