Gwamnatin jihar Kaduna ta hana yin taron bukukuwa na kowace iri da ake yi a ciki ko harabar makarantun firamare da sakandare na gwamnati.
Babban sakataren ma’aikatar ilimi na jihar Yusuf Saleh ya sanar da haka wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN.
Saleh ya ce gwamnati ta yanke wannan hukunci ne domin hana lalata kayan aiki na makarantun da mutane ke yi a lokacin bikin.
“Mafi yawan lokuta makarantun mu na yawan bukatan gyare-gyaren wanda haka ke sa ma’aikatar kashe kudi.
“A dalilin haka ya sa muka hana yin taron bukuwa a makarantun.
“Za mu aika da wasiku domin sanar wa Shugabanin makarantun firamare da na sakandare kan wannan mataki da gwamnati ta dauka.
Ya kuma ce nan ba da dadewa ba gwamnati za ta fara katange makarantun firamare da sakandaren da basu da katanga a jihar domin hana mutane shiga makarantun suna lalata kayan da ke makarantun.
Bayan haka Saleh ya ce ma’aikatar ilimi za ta hada hannu da ma’aikatar tsaro da harkokin cikin gida na jihar domin samar wa makarantun sakandare da firamare tsaron da ya dace a makarantun.
Shugaban hukumar KADBEAM Tijjani Aliyu ya jinjina matakin da gwamnati ta dauka sannan ya yi kira ga mutane da su hada hannu da gwamnati domin hana mutane lalata kayan makarantun gwamnati da aka kashe kudi aka saka.