Gwamnatin jihar Nasarawa ta hana siyarwa da amfani da gawayi a faɗin jihar wai domin kare muhalli.
Babban sakataren ma’aikatar muhalli da ma’adinai Aliyu Agwai ya sanar da haka wa manema labarai ranar a garin Lafia.
Agwai ya ce gwamnati ta dauki wannan mataki domin amfani da ake yi da gawayi wajen girke-girke da sauransu na daga cikin hanyoyin dake kawo illa ga muhalli da canjin yanayi.
“Sare itatuwa da ake yi domin samun gawayi na hana dabbobin dake daji samun wurin zama Wanda hakan ke kara cutar da muhalli.
Ya gargaɗi masu siyar da gawayi a jihar da su nemi wata sana’ar daga yanzu domin gwamnati za ta hukunta duk wanda ta kama yana siyar da gawayi a jihar.
Bayan haka Agwai ya yaba wa mazaunan jihar kan hadin kan da suka bada wajen kiyaye dokar tsaftace muhalli da gwamnati ta dawo da shi da ake yi ranar Asabar din kowace mako.
“Gwamnati ta dawo da dokar ne domin inganta tsaftace muhalli musamman a wannan lokaci da bukukuwan kirsimeti da na sabun shekara ya kunno kai.
“A wannan rana gwamnati kan hana kai-komon motoci tare da hana siye da siyarwa abubuwa irin haka domin karfafa gwiwowin mutane wajen tsaftace muhalli su.
Bayan haka kotu a lafia ta yanke wa mutum 32 hukuncin tarar naira ₦5000 zuwa ₦50,000 saboda karya dokar kasuwancin a lokacin da ake cikin dokar tsaftace muhalli na duka ranar Asabar a jihar.
Alkalin kotun Abdullahi Lande ya yanke wa mutanen hukuncin zama a kurkuku na tsawon watanni shida ko Kuma su biya taran Naira 5,000 zuwa 50,000.
Discussion about this post