Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar wa ƴan Najeriya cewa daga yanzu saura kiris a gama da Boko Haram kwata-kwata a jihar Barno da yankin Arewa Maso Gabashin Najeriya.
Idan ba a manta ba Jim ƙadan kafin saukar jirgin saman shugaba Muhammadu Buhari, mahara da ake zaton ƴan Boko Haram ɓangaren ISWAP ne suka yi wa garin Maiduguri ruwan bamabamai.
Duka unguwannin da bamabaman suka dira akan su na kusa da filin jirgin saman Maiduguri.
Unguwannin da abin ya shafa sun haɗa da unguwar Ayafe, Ajilari Cross, Moromti rukunin gidajena Legacy Housing estate dake Bulumkutu duk a cikin Maiduguri.
Rahotanni sun bayyana cewa akalla mutum 5 ne suka rasu a dalilin waɗannen hare-hare.
Shugaba Buhari ya zoyaci Maiduguri ne domin ƙaddamar da wasu manya ayyuka da gwamnatin jihar da aiwatar.
Buhari ya dira Maiduguri awa ɗaya bayan hare-haren da aka kai garin.
Baya ga manyan gadoji da Buhari zai kaddamar, akwai tituna da makarantu na zamani da zai kaddamar a jihar.
A jawabin da shugaba Buhari yayi, ya jinjina wa gwamnan jihar Barno Babagana Zulum kan ayyukan ci gaba da ya ke kantara wa mutanen jihar ta kowanne fanni.
Buhari ya yabi Zulum sannan ya yi kira ga gwamnoni su yi koyi da shi wajen samar wa mutanen jihar sa abubuwan cigaba da na more rayuwa.
Discussion about this post