Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa idan ya kammala mulki cikin 2023, zai koma gida Daura domin ya ci gaba da kula da garken shanun sa da ke can.
Buhari wanda zai kammala mulkin sa cikin 2023, lokacin ya na da shekaru 81 a duniya, ya bayyana haka ne a birnin Santanbul na Turkiyya, inda ya je can domin halartar taron haɗin-guiwa tsakanin wasu ƙasashen Afrika da Turkiyya, domin ƙarfafa cinikayya a tsakanin su.
Ya yi wannan furuci ne jim kaɗan bayan ya yanka kek ɗin murnar zagayowar ranar haihuwar sa, da kuma cikar sa shekaru 79 a duniya.
“Ina nan ina zuba ido, ina jiran da na sauka daga mulki cikin 2023, zan koma gida Daura, domin na ci gaba da kula da noma da kiwo na.” Haka Buhari ya shaida wa gungun ‘yan rakiyar sa, waɗanda ke tsaye tare da shi a lokacin da ya yanka kek ɗin, mai launin kore da fari da kore, wato launin tutar Najeriya.
Kafin zaɓen sa shugabancin ƙasa a 2015 dai Buhari ya na zaune ne a Kaduna.
Masu lura da al’amurran yadda ƙasar nan ta ke, su na ganin cewa da wahala Buhari ya koma Daura ya zauna, sai dai Kaduna.
Wannan jarida ta buga labarin cewa Buhari ya sake lulawa Turkiyya, lokacin da Arewa ke fama da kashe-kashen ‘yan bindiga.
Shugaba Muhammadu Buhari zai sake ficewa daga Najeriya zuwa Turkiyya, makonni biyu bayan ya dawo daga Afrika ta Kudu taron baje-koli.
Buhari zai je Turkiyya domin halartar taron haɗin guiwar ƙarfafa hulɗar cinikayya tsakanin Turkiyya da wasu ƙasashen Afrika.
Shugaba Racep Tayyib Erdogan ne ya shirya taron, bayan ziyarar da ya kawo cikin watan Oktoba a Abuja.
Za su tattauna batun ciniyakkar makamashi, tsaro, masana’antu da sauran su.
Shugaba Buhari na shan caccaka a Najeriya, inda masu adawa da yawan fitar da ke ganin cewa sagaraftu ne kawai ya ke yi da yawon gallafiri, a daidai lokacin da Arewacin Najeriya ke fama da kashe-kashen ‘yan bindiga.
Cikin wata biyu Buhari ya fice zuwa ƙasashe shida. Ya je Saudiyya, Ingila, Dubai, Scotland da kuma Afrika ta Kudu.
Yau kuma ranar Alhamis zai lula ƙasa ta bakwai, wato Turkiyya.
Jama’a da dama na ganin cewa kamata ya yi Buhari ya riƙa tura wakilcin Mataimakin Shugaban Ƙasa, Yemi Osinbajo, shi kuma ya zauna ya maida hankali wajen ganin tabbatar da zaman lafiya a Arewacin Najeriya da sauran yankunan ƙasar nan.
Discussion about this post