Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya yi wa iyalen matafiya 23 da ‘yan bindiga suka kashe a jihar Sokoto ta’aziyyar rasa ‘yan uwan su da suka yi.
Wasu gidajen jaridu sun rawaito cewa adadin yawan matafiyan da suka mutu a dalilin harin ya Kai 40.
Sai dai gwamnatin jihar Sokoto ta bayyana cewa mutum 23 ne suka mutu ba 40 ba.
Mai taimakawa gwamnan jihar Aminu Tambuwal, kan harkokin yada labarai Muhammad Bello ya tabbatar da haka a garin Sokoto.
“Mun samu labarin cewa ‘yan bindiga sun bude wa wata mota dake dauke da fasinjoji 42 za su Kaduna daga Sokoto ranar Litini a dai-dai kauyen Gidan Bawa dake karamar hukumar Isa inda a ciki mutum 23 suka mutu.
Bello ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar Kamaludeen Okunola ya tabbatar da haka wa gwamnati.
Ya ce motar ta kama da wuta bayan ‘yan bindigan sun buda matar wuta.
Bello ya ce zuwa yanzu akwai mutum shida dake kwance a asibiti da suka tsira da ransu daga harin.
Ya ce Tambuwal ya aika da sakon ta’aziyyar sa ga iyalen matafiyan da suka rasu a sanadiyyar wannan hari.
Shugaban ƙasa Buhari ya yi alhinin kisan matafiya da ‘yan bindigan suka yi a jihar.
Buhari ya ce jami’an tsaro za su ci gaba da kokari wajen ganin sun kawo karshen wannan matsala a kasar nan.
Discussion about this post