Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun sun kama Biodun Adebiyi mai shekara 32 da ya kashe wani mai tsaron shago saboda canjin naira 50 kudin karan sigari da ya siya.
Kakakin rundunar Abimbola Oyeyemi ya sanar da haka ranar Litini yana mai cewa rundunar ta samu labarin aika-aikan da Adeniyi ya yi bayan mahaifin mai siyar da sigarin Adamu Abubakar ya kawo karar a ofishin su dake Idiroko.
“A ranar biyar ga Disamba da misalin karfe biyu na rana Adebiyi ya siya sigari a hannun marigayi Mukaila Adamu mai shekara 30 dake jiran shagon mahafinsa Adamu Abubakar a Ajegunle dake Idiroko.
“Da misalin karfe 10 na dare sai Adebiyi ya sake dawowa shagon inda ya bukaci Mukaila ya bashi canjinsa Naira 50 na sigarin da ya siya da rana. Garin haka ne suka kaure da cacan baki a tsakanin su, shi kuma Adebiyi ya fusa ya dunkula hannu kuwa ya sheme Mukaila, nan take ya yanke jiki ya fadi nan take ya yayi sallama da duniya.
“Likitocin da suka duba shi bayan an kai shi asibiti sun shaida cewa ai gawa ce aka kawo asibiti domin Munkaila ya riga mu gidan gaskiya tun a lokacin da abokin fadan sa ya kifa masa naushi a lokacin da rikicin ya kaure.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Lanre Bankole ya ce an aika da fiyel din shari’ar fannin dake gurfanar da masu aikata laifuka irin haka domin ci gaba da gudanar da bincike.