An tabbatar da dace mahaifiyar Abdulkareem Asuku, wanda shi ne Shugaban Ma’aitakan Gidan Gwamnatin Jihar Kogi.
An yi garkuwa da mahaifiyar ta sa mai suna Seriya Raji daidai lokacin da ta kammala Sallar Isha’i daidai ƙarfe 7:40 a ranar Litinin, a cikin masallacin da ke gidan ta, wanda ke sabbin rukunin gidaje na Ovakere a unguwar Nagazi cikin Karamar Hukumar Adavi.
Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kogi, ya tabbatar da cewa jami’an sa da na sauran ɓangarorin tsaro sai sun ceto ta salum-alum, sun maido ta gida lafiya.
An ce maharan sun dira cikin gidan ta masallacin, kuma su shida ne, ɗauke da wata leda, wadda aka yi zargin bindigogi ne a cikin ta.
Sun tura matar a cikin motar da su ka je gidan da ita, kuma su ka arce. Har yanzu babu labari.
Ganau sun tabbatar da cewa mutanen da su ka tafi da mahaifiyar ta sa, dukkan su sanye su ke da hula wadda ta rufe fuskokin su.
Lamarin ya zo daidai lokacin da aka bada rahoton kisan wani jami’in lafiya da ‘yan bindiga su ka yi a Jihar Neja, bayan sun karɓi kuɗin fansa har naira miliyan takwas.
Yayin da ake ci gaba da kai samamen garkuwa da mutane, shi kuma Shugaba Muhammadu Buhari na ta ƙara tabbatar da cewa zai tsare rayuka da dukiyoyin jama’a.
Yanzu haka dai Buhari na shan caccaka a soshiyal midiya, bayan fitar wata sanarwa mai ɗauke da bayanan bikin naɗin ɗan sa Yusuf Buhari Talban Daura, wanda aka shirya za a gudanar a ranar 18 Ga Disamba, 2022