Kakakin majalisar Kaduna, Honarabul, Yusuf Zailani ya yi alhinin kisan ɗan majalisar dokokin jihar da ƴan bindiga suka yi ranar Litinin a hanyar Zaria-Kaduna.
Ƴan bindiga sun kashe matafiya da dama sannan sun sace wasu masu yawa a harin da suka kai titin Zaria-Kaduna ranar Litinin.
Cikin wanda aka kashe harda ɗan majalisan dake wakiltar Giwa a majalisar jihar, Honarabul Rilwanu Gadagau.
Zailani ya aika da ta’aziyyar sa ga iyalai da ƴan uwan mamacin kuma yayi fatan Allah ya kai rahama ƙabarin sa.
Wasu mazauna ƙauyukan da suka ga abinda ya auku sun bayyana cewa maharan ba su ɗaga wa kowa kafa ba.
” Ruƙugin fitar harsashi kawai muka rika ji, ƴan bindigan suna barin wuta, sun yi kan duk wani matafiya da ya biyo wannan hanya. Sun kashe na kashe wa sannan sun kwashi na kwashewa.
” Wannan hari ya yi matukar muni domin duk wanda ya faɗawa maharan a wannan lokacin bai tsira ba. Ko dai an tafi da shi, ko kuma sun kashe shi. Abin yayi muni matuka.
Kafin ya rasu, Gadagau ne shugaban kwamitin kula da ƙananan hukumomi na majalisar dokokin jihar Kaduna.
” Majalisar Kaduna ta yi babban rashi. Allah ya ji ƙan sa da waɗanda suka rasu.
Discussion about this post