Jakadar Birtaniya a Najeriya Catriona Lang, ta bayyana cewa Afrika, Birtaniya da duniya baki ɗaya sun zuba ido domin ganin yadda zaɓen 2023 zai kasance ko ya kakare a Najeriya.
Lang ta yi wannan furuci a taron zaburar da matasa fiye da 200 na yankin Kudu maso Yamma da su ka yanke shawarar shiga takarar muƙaman siyasa daban-daban a zaɓen 2023.
Kungiyar Yiaga da ‘Not Too Young to Contest’ ne su ka zaburar da matasan.
Lang ta ce an zuba-ido a ga shin za a gudanar da zaɓe sahihi? Za a bari a gudanar da zaɓe sahihi? Shin zaɓen zai zama karɓaɓɓe a zukatan waɗanda su ka jefa ƙuri’a ko kuwa?” Inji Lang.
Lang ta ce ya zama wajibi a Najeriya a bar matasa da mata masu yawa su tsaya takarar muƙaman siyasa, domin su ma a dama da su a dimokraɗiyya.
A wurin taron, Gwamnan Kwara ya ce gwamnoni ba su faɗa da Sanatoci a kan salon zaɓen-fidda-gwani.
Gwamna AbdulRazak na Jihar Kwara ya bayyana cewa babu wani gwamna ko gungun gwamnonin da ke rigima ko jayayya da sanatoci a kan salon zaɓen fidda gwanin jam’iyya.
Ya bayyana haka ne a wurin bayanin da ya yi wa taron matasa fiye da 200 waɗanda su ka nuna sha’awar fitowa takardar muƙaman siyasa daban-daban.
AbdulRazak ya ce babu ruwan sa da wani salon zaɓe, ko za na wakilai ko na ‘yar tinƙi, wanda doka ta ce shi za a yi, to ya na maraba da salon.
Matasan sama da 200 sun yanke shawarar shiga siyasa ne bayan da ƙungiyar Yiaga Africa da ‘Not Too Young To Contest’ su ka zaburar domin su shiga muƙaman siyasa a dama da su.
An samu bambancin ra’ayi tsakanin gwanonin Najeriya da sanatoci a kan salo da tsarin zaɓen fidda gwanin da jam’iyyun siyasa za su riƙa yi, wanda aka yi wa kwaskwarima a cikin Ƙudirin Gyaran Dokar Zaɓe, wanda a yanzu ke gaban teburin Shugaba Muhammadu Buhari, ana jira kawai ya sa masa hannu.
Yayin da gwamnoni ba su goyon bayan dokar da ta ce a soke yin zaɓe a ƙarƙashin wakilai, a koma ‘yar tinƙi, su kuma sanatoci sun nuna goyon bayan ‘yar tinƙen.
Zaɓen fidda gwani a ƙarƙashin wakilai shi ne wanda wakilan jam’iyya ke yi. Shi kuma ‘yar tinƙe shi ne wanda kowane ɗan jam’iyya mai ɗauke da katin rajista da jam’iyya ke da haƙƙin yin zaɓe.
Gwamnan Kwara ya ce wa matasan amma dai shi tsarin zaɓen daga wakilai ya kai shi tsayawa takara. Kuma ba ya tsoron ko ma wane irin salon zaɓe.
“Sai dai ku matasa a matsayin ku na farkon shiga siyasa, zaɓen fidda gwani a ƙarƙashin wakilai zai fi sauƙi wajen tsayawar ku takara.
Cikin wannan makon ne wannan jarida ta buga labarin cewa INEC ta aika wa Buhari wasiƙa amincewa da Ƙudirin Gyaran Dokar Zaɓe.
Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta aika wa Fadar Shugaban Ƙasa wasiƙar da batutuwan da Kudirin Gyaran Dokar Zaɓe ya ƙunsa.
Sai dai kuma INEC ta shawarci Shugaba Muhammadu Buhari ya tuntuɓi jam’iyyun siyasa da ɓangarorin jami’an tsaro, dangane da kudirin da aka shigar cewa zaɓen ‘yar-tinƙi jam’iyyu za su riƙa yi a wurin zaɓen fidda-gwanin ‘yan takara.
A ranar 29 Ga Nuwamba ce Majalisar Dattawa ta aika wa Shugaba Buhari Ƙudirin Gyaran Dokar Zaɓe, wanda shi kuma a bisa doka, ya na da kwanaki 30 kacal da zai ɗauka ya sa wa ƙudirin hannu, domin ya tabbata doka kenan.
Shi dai wannan sabon ƙudiri, matsawar Shugaba Buhari ya sa masa hannu, to ya shafe Dokar Zaɓen ta 2010 kenan, wadda ita ce aka yi wa kwaskwarima.
A cikin kwaskwarimar dai an nemi a riƙa yin zaɓen ‘yar-tinƙi wajen fitar da ‘yan takara.
Sai kuma batun suka sakamakon zaɓe ta yanar gizo da sauran na’urori da kafafen sadarwa na zamani.
Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Ibrahim Gambari ne ya rubuta wa INEC wasiƙa, inda ya nemi hukumar ta rubuto shawarwari ga Buhari, kan batutuwan da Kudirin Gyaran Dokar Zaɓe su ka ƙunsa.
Gambari ya shaida wa INEC cewa kada shawarwarin su wuce ranar 3 Ga Disamba.
Batun a koma yin zaɓen ‘yar-tinƙi wajen zaɓuka na fidda-gwanin takarar jam’iyyu ya haifar da ka-ce-na-ce a cikin jam’iyyar APC mai mulki. Yayin da ‘yan majalisa waɗanda mafi rinjaye ‘yan APC ne, su da ɓangaren Bila Tinubu ke goyon bayan ‘yar-tinƙe, su kuma yawancin gwamnoni sun fi so a bar tsarin yadda ya ke, wato wakilai tun daga mazaɓu har zuwa sama su riƙa yin zaɓen fidda-gwani.