Hukumar EFCC ta gurfanar da tsohon Babban Hafsan Sojojin Najeriya, Keneth Minima tare da wasu sojoji biyu, inda ta nemi kotu ta taka ruwan cikin su, domin su amayar da naira biliyan 13 da ta ce sun wawura, daga kuɗin sayen makamai.
An gurfanar da Minima tare da tsohon Babban Akawun Kuɗaɗen Sojojin Najeriya, Manjo Janar A. O. Adetayo da kuma wani Burgediya Janar R. I. Odi a Babbar Kotun Abuja.
Kafin Minima, Alex Badeh aka fara gurfanarwa kotu tuni, wanda ya taɓa riƙe muƙamin Babban Hafsan Tsaron Najeriya baki ɗaya.
Ana cikin shari’ar sa ne ya gamu da ajalin sa, inda aka yi masa kisan-gilla a cikin Disamba, 2018.
EFCC ta karɓi rahoton Kwamitin Binciken Kuɗaɗen Kwangilar Sayen Makamai A Cikin Hukumar Sojojin Najeriya, daga 2007 zuwa 2015.
Kwamitin dai na a ƙarƙashin shugabancin wani tsohon hafsan sojojin sama, mai suna Jon Ode.
A tsakanin 2010 zuwa 2015, “Hukumomin Sajan Najeriya sun karɓi maƙudan biliyoyin nairori daga hannun Gwamnatin Tarayya, domin sayen makaman yaƙi da Boko Haram. Amma kuma sai aka gano cewa duk manyan sojojin Najeriya ne su ka sace kuɗaɗen.”
Yadda Su Minima Su Ka Yi Wa Naira Biliyan 13 Haɗiyar Malmalar Tuwo:
Canje-canjen da ake yi wa su Minima sun nuna cewa wasu mutane da su ka haɗa da Laftanar Janar Kenneth Minima mai ritaya sun yi wa naira biliyan 13 da ɗoriya haɗiyar lomar tuwo.
Mutanen sun haɗa da Laftanar Janar Kenneth Minimah mai ritaya, kuma tsohon Babban Hafsan Sojojin Najeriya, Manjo Janar A.O Adetoyo, da Burgediya Janar R. I Odi.
“An lodi kuɗaɗen daga asusun ajiyar kuɗaɗen sojoji daban-daban, aka riƙa gabzawa cikin asusun ajiyar kamfanonin mutanen da ba su da alaƙa da cikin makamai ko wata harka a Hukumar Sojojin Najeriya.
Sai dai kuma lauyan waɗanda ake ƙara mai suna Mahmud Magaji, ya ce kwamitin bincike da ya miƙa wa EFCC rahoto, bai ce EFCC ta gurfanar da su ba, don haka ta yi riga-Malam-Masallaci.
Sannan kuma ya ce dukkan tsoffin sojojin a lokacin su na ƙarƙashin dokar hukunta ma’aikatan tsaro. Don haka sai dai a yi masu shari’a cikin gida ta jami’an tsaro, amma ba ta kotu ba.
Kotu ta ɗaga ƙarar zuwa ranar 9 Ga Disamba.
Discussion about this post