Jami’an ‘Yan Sanda a Jihar Imo sun kutsa cikin Cocin Saint Peter’s na mabiya dariƙar Angalika, su ka yi awon gaba da surikin tsohon Gwamnan Jihar Imo Rochas Okorocha, mai suna Uche Nwosu.
Ba a san takamaiman kama shi ɗin da aka yi kwanaki uku bayan rasuwar mahaifiyar sa ba, amma dai jami’in yaɗa labaran sa mai suna Darlington Ibekwe ya shaida wa wakilin mu cewa kafin su tafi da shi sai da su ka ɗan jijjibge shi tukunna. Sannan kuma ya ƙara da cewa sun ci mutuncin sa, ta hanyar ci masa kwala, har ma da gaura masa mari.
“Mu na cikin coci sai ga motoci uku ɗauke da ‘yan sanda. Mota ɗaya Hilux ce, ɗaya Hyundai ce fara, ɗayar kuma Ford Explorer ce.
“Sun shigo sun nemi ya tashi ya bi su. An ci masa kwala sannan aka kifa masa mari. Aka ce ya tashi a tafi da shi.
“Sun mari surikar sa Nkechi, matar Sanata Okorocha, kuma sun tozarta Uloma, matar Nwosu kuma ‘ya ga Okorocha. Don kawai sun tambayi inda za su tafi da Nwosu.
“Sun ci kwalar sa aka riƙa jan sa har cikin mota. Sannan kuma su ka riƙa harba albarusai a sama don su firgita mutanen da ke kewaye da kuma cikin cocin.
Nwosu dai ya yi takarar gwamna a zaɓen 2019.
PREMIUM TIMES ta tuntuɓi Kakakin Yaɗa Labaran ‘Yan Sandan Jihar Imo, Mike Abbatam amma ya ce ba shi da labarin cewa yan sanda sun kama Nwosu.
Darlington dai ya ce jami’an sun ce daga Abuja aka aiko su.