Daruruwan ƴan kasuwan kofar Wambai sun yi cincirindo a layin Sani Buhari dake cikin kasuwar domin yin zanga-zangar nuna rashin jin daɗin su ga karin shaguna da gwamnati ta ke a kasuwar.
Ƴan kasuwan sun koka cewa wannan wuri dai za a gina shi me don son kai ba don taimakon talakawa ba.
” Wannan wuri dai hanyar wucewa ce, idan aka gina shaguna kamar yadda gwamnati ke yi yanzu haka cinkoso kawai za su kawo a kasuwar sannan akwai waɗanda anan gefe haka suke sana’ar su duk za a tada su kenan.” In ji wani ɗan kasuwa.
Da yawa daga cikin waɗanda suka tattauna da wakilinmu a Kano su bayyana cewa wannan aiki muzguna musu gwamnati ke son ta yi kuma ba za su hakura ba za su ci gaba da yin zanga-zanga har sai gwamnati ta dakatar da aikin.
” Wannan aiki ne kawai don wasu su samu kuɗi don kansu amma ba wai don taimakon kasuwar ba. Idan ma gwamna bai sani bane to lallai muna kira ya sani ba za mu amince da haka.
” Kiri kiri ga shi nan har harbe harben bindiga ƴan sanda suke yi sama don su bamu tsoro amma ba za mu tsorata ba. Wannan aiki ba don ci gaban talaka bane aiki ne na son rai da tozarta talaka kawai, wannan shine gaskiyar magana.
Discussion about this post