Sanata Ɗanjuma Goje wanda kamar shine maigidan duk wani ɗan siyasa a jihar Gombe ya tsallake rijiya da baya ranar Juma’a a garin Gombe inda wasu ƴan takife suka afka wa jerin gwanon motocin sa da makamai har aka yi sare-sare.
Majiya ta shaida wa PREMIUM TIMES HAUSA cewa an daɗe ana takun saƙa tsakanin ɓangaren gwamnan jihar da na sanata Goje kan wanene ke babban limamin siyasa a jihar Yanzu,
Idan ba a manta ba, gwamnatin jihar Gombe ta zargi sanata Goje da ingiza yaran sa su tada husuma a lokacin bikin babbar sallar bara da yayi sanadiyyar mutuwar mutum biyu.
Rahotanni sun nuna cewa a yamutsin ranar Juma’a mutum 5 sun sheka lahira sannan wasu da dama sun ji rauni.
A sanarwar da fadar gwamnatin jihar Gombe ta fitar, da farko dai ta yi Allah-wadai ne da abinda ya faru a lokacin ziyarar Goje garin Gombe.
Cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na Jihar Julius Ishaya Lepes ya fitar ya ce tsohon gwamna Goje ya taho da gungun ƴan daba ɗauke da makamai su yi masa rakiya daga filin jirgi da ya sauka garin Gombe.
Sai dai Sanata Goje shi ma ya fitar da sanarwa kan lamarin inda yake cewa gwamnati ta tura ‘yan sanda su ka tare masa hanya da kuma kai hari kan jerin gwanon motocinsa, lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa daurin auren jikarsa.
Sanarwar da mataimakiyarsa ta musamman kan harkokin yada labarai Lilian Nworie, ta fitar ta ce mutam daya ya mutu yayin wannan hatsaniya, abin da bai yi wa Sanata Goje dadi ba.
Amma gwamnatin jihar ta ce mutum biyar ce suka mutu a bayanan da ta samu ya zuwa yanzu.