Hukumar EFCC ta sake gurfanar da tsohon Ministan Kimiyya da Fasaha Abdu Bulama a kotu, bisa zargin sa da yin harƙallar naira miliyan 450.
Cikin wata sanarwar da Kakakin EFCC, Wilson Uwujaren ya fitar, ya bayyana cewa an sake gurfanar da shi a ranar Litinin a Babbar Kotun Tarayya da ke Damaturu, Jihar Yobe.
An sake gurfanar da Bulama tare da tsohon Kwamishinan Inganta Karkara na Jihar Yobe, Mohammed Kadai, sai Abba Tata, Muhammad Mamu da Hassan Jaks.
Ana zargin tsohon ministan da karɓar Naira miliyan 450 daga hannun tsohuwar Ministar Harkokin Fetur, Diezani Allison Maduekwe, domin yin amfani da kuɗaɗen wajen toshiyar bakin cin zaɓe ga PDP a zaɓen Shugaban Ƙasa na 2015.
A zaɓen 2015 dai Bulama shi ne kodinetan kamfen ɗin Shugaba Goodluck Jonathan na jihar Yobe a lokacin.
Yayin da Kadai ke Mataimakin Kodinetan Yobe, sauran mutanen uku kuma duk mambobin kwamiti ne.
EFCC ta ce sun karya Dokar Ƙasa ta Sashe na 18(a) ta Kuɗaɗen Zamba da Haramcin Kuɗaɗen Zamba, ta shekarar 2011.
Mai Shari’a ya bada belin kowanen su kan kuɗi Naira miliyan 50. Amma ya kasance kowanen su mutane biyu ne za su tsaya masu beli, kan Naira miliyan 25 kenan kowane mutum ɗaya.
Mai Shari’a Aminu ya ɗaga sauraren ƙarar zuwa ranakun 18,19 da Ga Janairu, 2022 domin fara shari’ar.
Sai dai kuma ya bai wa EFCC umarnin ƙwace masu fasfo har sai abin da hukuncin kotu ya kama.