Cikin daren ranar Laraba ce ‘yan bindiga suka kutsa garin Tungar Ruwa suka kashe Dagacin garin da kuma wasu makusantan sa su takwas.
Mummunan lamarin ya faru a cikin Ƙaramar Hukumar Anka da ke Jihar Zamfara.
Kakakin ‘Yan Sandan Zamfara Mohammed ya tabbatar wa PREMIUM TIMES faɗuwar lamarin, a lokacin da wakilin mu ya kira shi domin jin tabbaci.
Karamar Hukumar Anka na cikin ƙananan hukumomin da ‘yan bindiga ke ci gaba da cin karen su ba babbaka a jihar Zamfara.
Da yawan mazauna ƙauyukan yankunan Anka, Maru da Talata Mafara sun yi gudun hijira daga ƙauyuka, sun koma cikin hedikwatar ƙaramar hukuma, wato cikin garuruwan Maru da Anka da Talata Mafara.
Wani mazaunin Anka mai suna Anas Mustapha, ya shaida wa wakilin mu cewa maharan sun je ne a kan babura, inda kai tsaye suka tunkari gidan basaraken garin su na harba bindigogi a sama.
“Sun kutsa cikin gidan Dagacin su ka fito da shi sannan suka yi masa yankan rago a gaban jama’a.”
PREMIUM TIMES ta kuma ji cewa an yanka wasu mutum takwas bayan yanka Dagacin.
“Ka san su ‘yan bindiga matsawar suka gano ka na kawo masu matsala, to nan da nan sai su kashe mutum kawai.” Inji Mustapha.
Maharan sun sace abinci da dabbobi, amma ba su riƙe ko mutum ɗaya ba.
Wannan mummunan kisa ya faru ne kwanaki kaɗan bayan da wasu ‘yan bindiga su ka yi wa ‘yan sandan ‘Mobal’ kwanton-ɓauna, har su ka kashe takwas cikin su.
Discussion about this post