Gwamnatin jihar Zamfara ta bayyana cewa za ta buɗe kasuwannin da ake ci duk mako guda bakwai a jihar.
Kwamishinan yaɗa labarai Ibrahim Dosara ya sanar da haka ranar Litinin a garin Gasau.
Dosara ya ce ganin dawowar zaman lafiya da aka samu a wasu yankunan jihar ya sa gwamnati ta yanke hukunci buɗe waɗannan kasuwanni a jihar.
Ya kara da cewa waɗannan kasuwanni za ta bude za su fara aiki ranar Litini daya ga Nuwanba.
Kasuwannin da za a buɗe sun hada da;
Nasarawar Burkullu dake karamar hukumar Bukkuyum,
Talata Mafara dake karamar hukumar Talata Mafara, kasuwan Gusau dake karamar hukumar Gusau, kasuwan Shinkafi dake karamar hukumar Shinkafi.
Saura sun hada da Kasuwar Daji dake Kaura Namoda, Nasarawar Godel dake karamar hukumar Birnin-Magaji da kasuwan Danjibga dake karamar hukumar Tsafe.
Gwamnati ta kuma saka wasu sharuɗɗa wanda idan ba a kiyaye ba za ta sake rufe kasuwannin.
Ga sharuɗɗan
1. Ba za a Rika siyar da dabobbi ba a kasuwannin
2. Kada a shiga kasuwa da makami kowani iri.
3. Gwamnati ba ta amince wasu mutane ko Kungiya su rika shiga kasuwannin suna cin zarafin mutane ba.
4. Gwamnati ta saka jami’an tsaro da za su tabbatar mutane sun kiyaye wadannan dokoki da aka saka.
Discussion about this post