Wani jigon Jam’iyyar PDP mai suna Lawal Usman, ya ce idan har PDP na so ta kai labari, to tilas fa sai ta bayar da takara ga Arewacin Najeriya, saboda waɗansu ƙwararan dalilai.
Usman, wanda aka fi sani da Mr LA, ya yi wannan furuci a lokacin ganawar sa da manema labarai a Zariya, a ranar Lahadi.
“Saboda wasu dalilai ga ita kan ta jam’iyyar da kuma ƙasa baki ɗaya, mafitar PDP kawai ita ce a bai wa ɗan Arewa takardar shugabancin ƙasa a zaɓen 2023.” Inji shi.
Usman ya ce tilas PDP ta yi adalci da kuma dattako ta bayar da tikitin takara ga ɗan Arewa.
“PDP ta riƙe mulki shekaru 16, waɗanda daga ciki Kudu maso Yamma ta riƙe shekaru takwas a ƙarƙashin Obasanjo. Kudu maso Kudu ta riƙe shekaru shida a hannun Jonathan.
“Gaba ɗayan Arewa tun daga Arewa ta Tsakiya, Arewa maso Gabas, ba su yi ko mulkin raba ɗaya ba. Sai Arewa maso Yamma ce ta yi mulkin shekaru biyu kacal, a ƙarƙashin marigayi Umaru ‘Yar’Adua.” Inji Lawal.
Usman wanda ya taɓa yin takarar sanatan Kaduna ta Tsakiya, ya ce jam’iyyar PDP ta fi kowace jam’iyya yawan magoya baya a Arewa.
Discussion about this post