Ana can ana shirye-shiryen zaɓe a Jihar Anambra, inda mutum miliyan 2.5 ne su ka yi rajistar zaɓe.
Yayin da jam’iyyu 18 ne su ka shiga takara, amma dai an fi ganin samun nasara tsakanin ‘yan takara uku, wato Charles Soludo na APGA, Andy Uba na APC da kuma Valentine Ozigbo na PDP.
Yawan jama’a a jihar Anambra ya kai mutum miliyan 4.
Akwai ƙananan hukumomi 21 a Jihar Anambra, yayin da akwai rumfunan zaɓe 5,720.
Sai dai kuma INEC ta ce ba za a yi zaɓe a rumfuna 80 ba, saboda babu waɗanda suka yi rajista a rumfunan.
Dukkan waɗannan manyan ‘yan takara uku dai kowa na ganin shi ke da nasara, tun ba a kai ga jefa ƙuri’a ba.
Duk da dai APGA wadda ita ce jam’iyya mai mulki, ta zaizaye sosai, har mataimakin gwamna ya koma APC.
Valentine Ozigbo na PDP dai shi ma ya shirya, amma ana ganin ba zai iya kayar da Soludo na APGA ko Andy Uba, mai uwa a gindin murhu ba.
Ƙaƙa-tsara-ƙaƙa!
Discussion about this post