1. Ganin yadda aka riƙa samun tsaiko da jinkirin isar kayan zaɓe da jami’an zaɓen su kan su a wasu rumfunan zaɓe, jam’iyyar APC da PDP sun riƙa ɗaukar shatar ‘yan kabu-kabun acaɓa su na jigilar malaman zaɓe da kayan zaɓe zuwa wasu mazaɓun da ba a kai kayan aiki da wuri ba.
2. Duk da Gwamnatin Tarayya ta jibge ‘yan sanda har 40,000 a Jihar Anambra domin bayar da tsaro yayin zaɓe, wakilan mu su tabbatar da cewa har zuwa bayan ƙarfe 12:30 na rana, babu jami’an tsaro a wasu rumfunan zaɓe.
3. Shugaban Ƙungiyar Masu Sa-ido Kan Zaɓe wato Nigerian Civil Society Situation Room, Ene Obi, ya tabbatar da cewa da rana jama’a sun riƙa fitowa sosai domin su jefa ƙuri’a. Ba kamar da safe ba, inda jama’a duk aka yi likomo a gida.
4. Mataimakin Gwamna Nkem Okeke ya fita ya je ya jefa ƙuri’a. Kuma ya bayyana gamsuwar sa dangane da yadda zaɓen ke tafiya.
5 – Wakilan jam’iyyu sun rika bin masu zaɓe suna cinna musu dammai, wato nairori.
6 – Wasu wuraren dai har yanzu masu zaɓe basu kai ga garzaya kaɗa kuri’a ba, wasu kuma na’urorin ne suka ki aiki