Hukumar Zaɓe ta Ƙasa ta bayyana cewa za a yi zaɓen da ta ce bai kammalu ba a ranar Talata, 9 Ga Nuwamba.
A ranar Lahadi Babbar Jami’ar Zaɓe, Florence Obi ta bayyana cewa zaɓen ya zama ‘inkwankulusib’, saboda ba a samu damar yin zaɓe a Ƙaramar Hukumar Ihiala ba.
Ƙaramar Hukumar Ihiala na da waɗanda ke da rajista har mutum sama da 148,000, kamar yadda Obi ta tabbatar wa manema labarai.
Ta ce ba a samu gudanar da zaɓe a Ihiala ba, saboda matsalar kai kayan zaɓe da malaman zaɓen.
Saboda haka ne ba ta bayyana sakamakon zaɓen wanda ya yi nasara ba, har sai an ƙidaya ƙuri’un zaɓen da za a yi a Ihiala tukunna.
Yanzu dai Charles Soludo na jam’iyyar APGA ke gaba da ƙuri’u 103,946. Wanda ke masa Valentine Ozigbo na da ƙuri’a 51,323.
Soludo ya lashe ƙananan hukumomi 18 daga cikin 20 ɗin da aka bayyana sakamakon su.
Charles Soludo wanda ya lashe ƙananan hukumomi 18 cikin 20 da aka bayyana sakamakon su, ya sha kaye a Ƙaramar Hukumar Ogbaru, inda can ne mahaifar Minista Stella Odua.
Sai dai kuma abin mamaki, ɗan takarar jam’iyyar PDP, Valentine Ozigbo ne ya kayar da shi, ba Andy Uba, ɗan takarar APC jam’iyyar su Stella ɗin ba.
Yayin da Ozigbo ya samu ƙuri’u 3,445, Soludo ya samu 3,051.
Tuni dai duk da kurin da Andy Uba yya riƙa yi, Soludo ya tsere masa fintinkau da ƙuri’a kusan 60,000.
Jihar Anambra ita ce jihar ta biyu wajen ƙankantar faɗin ƙasa a Najeriya.
Jihar Legas ce kaɗai ta fi jihar Anambra faɗi.
Discussion about this post