Da misalin ƙarfe 9:28 daidai ne Gwamna Willie Obiano na Jihar Anambra, kuma ɗan jam’iyyar APGA ya isa rumfar zaɓe mai lamba PU004, a unguwar Otuacha 1, Aguleri cikin Ƙaramar Hukumar Anambra ta Gabas.
Ya isa tare da matar sa mai suna Ebelechukwu, kuma da fitar da mota, sai ya tafi ya shiga layin masu tantance masu zaɓe.
Bayan minti biyar ya na tsaye, hadiman sa sun yi masa iso cewa ya je ya jefa ƙuri’a.
Obiano ya yi kira ga al’ummar jihar Anambra cewa duk mai rajista ya gaggauta fitowa ya jefa ƙuri’a.
A daidai lokacin da Gwamna Obiano ya kaɗa ƙuri’a, can a garin Achalla da ke ƙaramar hukumar Awka kuwa, bidiyo ya nuno malaman zaɓe da jami’an tsaro sun yi cirko-cirko, saboda rashin motar da za ta kwashe su da kayan aikin su zuwa rumfunan da aka tura su aikin zaɓe.
Sannan kuma su na jin haushin ƙin biyan su kuɗaɗen alawus ɗin cin abinci da ba a yi ba.