Ɗan takarar gwamnan Jihar Anambra na APC a zaɓen ranar 6 Ga Nuwamba, Andy Uba, ya ƙi amincewa da nasarar da Chukwuma Soludo na APGA ya yi a zaɓen.
Kakakin Tawagar Kamfen ɗin Andy Uba mai suna Jerry Ugokwe ne ys bayyana haka a cikin wata sanarwar da ya fitar ranar Alhamis a Abuja.
Uba ya ce zaɓen shirme ne, shiririta kuma wasan kwaikwayo ne, wanda ba a hasko haƙiƙanin abin da jama’ar Jihar Anambra su ka dangwala wa ƙuri’a ba.
Andy Uba dai ya zo na uku da yawan ƙuri’u 40,000 da ‘yan ɗoriya, yayin da tsohon gwamnan CBN Charles Soludo ya zo na ɗaya da ƙuri’u 113,000.
Ugokwe ya ce an yi wa Andy Uba maguɗi. “An haɗa baki da INEC da jami’an tsaro da gwamnatin Willie Obiano ta APGA a Jihar Anambra, aka yi wa ɗan takarar APC Andy Uba maguɗi.
“Ba zai yiwu a ce ɗan takarar mu da ya samu sama da ƙuri’u 200 a zaɓen fidda-gwamnin APC, amma a ce ya tashi da ƙuri’u 43,000 kacal a zaɓen gwamna sukutum ba.”
Premium Times Hausa ta buga bayanin Kwamishinan Zaɓen Anambra, inda ya ce “zaɓen Gwamnan Anambra ne zaɓe mafi wahalarwa da na taɓa fuskanta.
Kwamishinan Zaɓe na Jihar Anambra, Samuel Egwu ya bayyana rashin gamsuwa sa da zaɓen gwamnan jihar Anambra da aka yi a ranar Asabar, wanda INEC ta bayyana cewa bai kammalu ba.
A wata tattaunawa da aka yi da shi a gidan talabijin na Channels, a ranar Lahadi, Egwu ya ce “wannan ne zaɓe mafi wahalarwa kuma cukurkuɗaɗɗen da ta taɓa fuskanta.”
Kwamishinan zaɓen ya ce babbar matsala ta farko da ta fi samun sa, ita ce rashin fitowar masu jefa ƙuri’a a mazaɓu da rumfunan zaɓe da dama. Hakan kuwa inji shi, ba abin alheri ba ne ga dimokraɗiyyar Najeriya.
“Na fara aiki da Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) cikin 2017. Kuma tun daga lokacin na shiga aikin shirya zaɓe sau dama. Amma ina tabbatar da cewa wannan zaɓen na gwamnan Anambra shi ne mafi wahalarwar da na taɓa fuskanta.”
“Tun daga jiya Asabar mu ka fuskanci babbar matsalar rashin fitowar masu rajistar zaɓe su jefa ƙuri’a.”
Egwu ya danganta rashin fitowar masu jefa ƙuri’a da tsaron barazanar da IPOB suka yi cewa kada wanda ya kuskura ya fito yin zaɓe a ranar Asabar.
Duk da dai a jajibirin zaɓe IPOB ta fitar da sanarwar janye dokar hana mutane fita da ta ƙakaba, hakan bai sa an fito dafifi an jefa ƙuri’a ba.
Rahotanni da dama sun nuna cewa kashi 20 bisa 100 kaɗai ne na masu rajistar zaɓe su ka jefa ƙuri’a.
Egwu na nuna matuƙar damuwar sa ganin yadda jama’a ba su fito sun jefa ƙuri’a sosai a ƙananan hukumomi uku da ya yi aikin sa-ido, wato Abacha ta Arewa, Anacha ta Kudu da kuma Ƙaramar Hukumar Ogbaru.
“A ƙananan hukumomin, masu rajista sun kai 14,000 ko ma 15,000. Amma waɗanda aka tantance a ranar zaɓe ba su tsakanin 1,200 zuwa 1,500 kacal ba.”
Da ya ke magana kan matsalar raba kayan zaɓe, Egwu ya ce an samu matsaloli a wasu yankuna ne saboda waɗansu da aka ɗauka aikin sun janye jikin su a jajibirin zaɓe.