Wasu ‘Yan Bindiga sun yi wa mutum 15 kisan gilla a kananan hukumomin Goronyo da Illela dake Jihar Sokoto.
Gwamna Aminu Tambuwal shi ne tabbatar da faruwar harin a inda yace an kashe mutum 12 a Illela sai kuma mutum uku da suka rasa rayukansu a Goronyo.
Tambuwal ya bayyana hakan ne jim kadan kafin ya gabatar da kasafin kudi na shekarar 2022 a majalissar dokokin Jihar.
Yace harin ya auku ne a ranar Lahadi zuwa safiyar Litinin a garuruwan guda biyu. Ya kuma jajintawa iyalan wadanda suka rasa rayukansu a wannan harin.
Kananan hukumomin Illela da goronyo inda aka kai harin suna cikin jerin kananan hukumomi da gwamnati ta datse wayar sadarwa saboda dakile ayyukan yan bindiga.
Duk da matakan da gwannati ta dauka, ‘Yan Bindiga da ‘yan sakai (vigilante) suna cigaba da kashe mutune babu kaukatawa a wasu yankuna na Jihar Sokoto.
Rohotanni sun nuna cewa Yan Bindiga suna sanya doka da karbar a haraji a wasu yankuna na Jihar Sokoto.
‘Yan bindigan sukan saka kudade a matsayin haraji ga gidajen mutane su rika biya.
Mazauna wasu kauyukan jihar sun koka cewa haka kowa ke fama da matsalar ‘yan bindiga a yankin.
“Idan suka saka harajin dole a biya domin har kunne su ja wa mutane lallai su biya ko kuma mutum ya bakonci lahira.
Discussion about this post