Wani direban motan haya a jihar Ebonyi ya gutsire yatsan wani jami’in duba gari sannan ya hadiye yatsan bayan rikici ya kaure tsakanin su a tashan mota a Abakaliki.
Wannan jami’i dai daya ne daga cikin duba gari na hukumar kula da birane na jihar dake kula da yadda ake ajiye motoci da hana cinkoso a manyan titunan jihar.
An bayyana cewa rikici ne ya kaure tsakanin direban motan hayan da jami’in da ya nemi ya kama shi, garin kokuwar fizgewa daga hannun jami’in sai direban motan hayan ya gantsara masa cizo a dan yatsa.
Cizon bai isheshi ya guntile hannun sannan maimakon ya ya jefar da dan yatsan sai sai kawai ya taune ya hadiye sannan ya ja motar sa ya gudu.
Kwamishinan tsare-tasre da raya birane na jihar Ebonyi din, ya yi tir da wannan abu da ya auku da jami’in ma’aikatar yana mai cewa wannan abu abun tsoro ne da ban mamaki.
” Ace wai mutum ya kama hannun wani dan wansa ya gutsire sannan ya cinye ba abinda hankali zai dauka bane. Sannan kuma shi jami’in yana wurin aikin sa ne.
Tuni dai har an garzaya da wannan jami’i asibiti ana yi wa sauran rauwar yatsar aiki.
Discussion about this post