Wani magidanci mai shekaru 39, Jamilu Idris ya bayyana wa rundunar ‘yan sandan jihar Katsina yadda ya sace dan kawun sa, ya kuma nemi a biya kudin fansa kafin dubu ta cika.
Idris ya ce” Na yi tattaki ne har zuwa Funtua garin da Kawu na ke zaune. Da na isa gidan sa sai shi wannan yaro ya fito cikin fara’a a don ya san ni kawun sa ne ya ce min baba ba ya nan. Sai na ce masa ya zo ya raka ni.
” Na siya masa madarar Viju sannan muka nausa tashar mota muka hau motar Abuja. Da muka isa Abuja sai na kai shi gidan wata mata na yi mata karyar dan abokina ne ya yi tafiya.
” A haka ne fa na samu waya na kira mahaifin sa, na canja murya na yi kamar bafulatani ne ke magana. Na ce masa mun sace yaron sa, yanzu ya kawo mana naira miliyan biyar kudin fansa kafin mu sake shi. Sai yayi ta roko bashi da miliyan biyar sai naira 500,000.
Mahaifin yaron sai ya garzaya ofishin yan sanda ya sanar da su abin da ake cike. daga nan sai suka fantsama bincike da farautar Jamilu, wanda ya sace dan uwan sa.
A karshe dai yan sanda sun hori mutane da su rika sanar da jami’an tsaro idan irin wannan tsautsayi ta afka musu.
Discussion about this post