Akalla mutum 13 ne ‘yan bindiga suka kashe a harin da suka kai garin Batsari jihar Katsina ranar Talata da yamma.
Ƴan bindigan sun yi garkuwa da mutum 17 a wannan hari da suka kai kuma mutum 8 sun ji rauni.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Gambo Isa ya ce mutum 11 ne ‘yan bindigan suka kashe a garin amma mazaunan garin sun ce mutum 13 ne aka kashe.
Dan majalisar dokoki na jihar da ke wakiltar Batsari Jabir Yau Yau ya tabbatar da harin sai dai ya ce bashi da masaniyar yawan mutanen da aka kashe a garin.
Yau ya ce zai sanar wa wakilin PREMIUM TIMES da zaran ya je garin ya gudanar da bincike.
Bayan haka wani mazaunin garin Abubakar Bishir ya ce sun yi jana’izar mutum 13 ranar Laraba da karfe 10 na safe.
Isa ya ce maharan sun afka garin da misalin karfe 7:15 na yamman Talata ne.
“Maharan sun shigo a lokacin mutane na sallah inda suka kan mai uwa dawabi bindigar su. A dalilin haka mutum 11 sun mutu sannan mutum 8 sun ji rauni a jikinsu.
Wani mazaunin garin Mukhtar Mamman ya ce maharan sun dauki awowi a cikin garin suna aikata abinda suka ga dama.
Sun rika shiga gidajen mutane suna satar abinci.
Mamman ya ce wadanda suka ji rauni na kwance a asibitocin Batsari da Katsina likitoci na duba su.
Batsari gari ne dake kusa da dazukan Rugu da Jibia.