A ranar Alhamis din makon jiya ne Boko Haram suka saki wani ma’aikacin gwamnatin jihar Yobe Ali Shehu wanda aka fi sani da sunan Mai Lalle da abokinsa Mustapha
Masu garkuwa da mutanen sun yi garkuwa da wadannan mutane tare da wasu sojoji biyu ranar 24 ga watan Yuli a hanyar Maiduguri zuwa Damaturu.
An samu labarin cewa masu garkuwa da mutanen sun kashe wadannan sojoji biyu daga baya.
Shehu da abokinsa Mustapha sun dawo gida sai dai anyi ta cewa wai sai da aka biya makudan kudade kafin aka sake su.
Wani cikin ‘yan uwan Shehu da baya son a fadi sunan sa saoda tsaro ya tabbatar wa PREMIUM TIMES cewa sai da aka kai Shehu da Mustapha asibiti kafin suka dawo gida. Sai dai bai fadi ko an biya kudin fansa ba.
” Kai dai kawai Allah dai ya tsare ya ci gaba da kare mu daga shiga hannun Boko Haram domin abin da ya samu mutanen nan ko kai ba za kaso hakan ya sami makiyin kaba.