Wasu ma’aikatan karamar hukumar Zaria su 13 sun faɗa hannun wasu ƴan bindiga a hqnyar su na zuwa ta’aziyyar rasuwar mahaifin wani abokin aikin su a karamar hukumar giwa jihar Kaduna.
Giwa na da nisan akalla kilomita 100 daga Zaria sannan yana cikin garurruwan da mahara suka addaba a jihar Kaduna.
An yi garkuwa da ma’aikatan ne ranar Litini yayin da suke hanyar zuwa ta’aziyyar rasuwar mahaifin wani abokin aikin su.
Hajiya Dalhat wacce ƴar uwar ɗaya daga cikin wanda aka sace ne, Suleiman Zailani, ta bayyana wa PREMIUM TIMES cewa har yanzu maharan basu tuntuɓi ƴan uwan waɗanda aka sace ba.
“Direban motar da ma’aikatan ke ciki ne ya dawo da sakon wai mahara sun sace ma’aikatan.
Direban ya ƙara da cewa maharan sun sake shi ne saboda ya sanar da iyalen ma’aikatan abin da ya faru da su.
Dalhat ta ƙara da cewa direban ya ce sun bace a hanya sai suka tambayi wasu hanyar da za su bi.
“Da gangar mutanen suka nuna mana hanyar da ta kaimu ga ƴan bindigan.
Gaba dayan su kaf ƴan bindigan suka sace kum har yanzu ba a samu wani bayani daga garesu ba tukunna game da ko za a biya su kuɗin fansa ko kuma a’a, sannan kuma ko jami’an tsaro sun fantsama neman su.