Shugaban Jami’ar Abuja AbdulRasheed Na’Allah ya sanar cewa an sako mutum shidan da ƴan bindiga suka yi garkuwa da su a jami’ar ranar Talata.
Idan ba a manta ba a ranar Talatan da ta gabata ƴan bindiga sun yi garkuwa da mutum shida daga jami’ar ciki har da wani farfesa mai suna, Obansa Joseph da ‘ya’yan sa biyu.
Farfesa Obansa Joseph yana karantarwa ne a sashen koyar da Tsimi da Tattali wato Economics a jami’ar sannan ‘ya’yan sa biyu da aka sace ba a fadi sunayen su ba.
Na’Allah ya kara da cewa ƴan bindigan sun bukaci a biya su Naira miliyan 300 kafin su saki mutanen da ke tsare a hannun su amma Jami’ar bata biya ko sisi ba.
“An ceto wadannan mutane a dalilin hada hannun da jami’an tsaro na SSS, sojoji da jami’an tsaron jami’ar su kayi ne.
Na’Allah ya mika godiyar sa ga mutane na addu’o’i da goyon baya da suka baiwa jami’ar a yi lokacin da wannan abu ya auku.
Ya kuma mika godiyarsa ga jami’an tsaron da suka ceto wadannan mutane.
Na’Allah ya ce Jami’ar za ta inganta tsaro domin hana maimaicin ukuwar haka nan gaba.
Tuni har kowa ya koma ga iyalan sa, kamar yadda mahukuntan jami’ar suna bayyana.