A daren Lahadi ne ‘yan bindiga suka kai farmaki kauyen Kwarin Mai Saje dake karamar hukumar Tsafe jihar Zamfara saboda mazauna kauyen sun kasa biyan Naira miliyan uku kudin harajin da ‘yan bindigan suka saka musu.
‘Yan bindigan sun yi wa mata fyade, sun saci kayan mutane masu daraja sannan suka yi garkuwa da akalla mutum shida a wannan kauyen.
Dama ‘yan bindigan sun saka wa kauyuka 13 banda kauyen Kwarin Mai Saje a karamar hukumar Tsafe su
rika biyan haraji.
Daga baya wasu maharan dake tare da Ada Aleru suka saka wa Kwarin Mai saje biyan haraji har Naira miliyan uku makonni biyu da suka gabata.
Wani mazaunin garin Sama’ila Tsafe yace rashin biyan harajin ya sa maharan suka kawo musu hari ranar Lahadi.
“Ba wai ba za a biya kudaden da suka ce a biya ba amma rashin kudi ya hana a biya kuɗaɗen.
“Har an tara Naira 600,000 daga cikin Naira miliyan uku din da suka ce a biya sannan mazaunan kauyen sun nemi taimakon mutane daga waje domin su samu su cika kudaden amma basu samu ba.
Tsafe yace maharan sun kawo wa kauyen farmaki domin wai ya za ma darasi ga sauran kauyukan da za suke tunanin kin biyan harajin.
Duk da matakan da gwamnati ta dauka, ‘Yan Bindiga da ‘yan sakai (vigilante) suna cigaba da kashe mutune babu kaukatawa a wasu yankuna na Jihar Zamfara.
Rohotanni sun nuna cewa ‘yan bindiga suna sanya dokan karban haraji a wasu yankuna na Jihar Zamfara.
‘Yan bindigan sukan saka kudade a matsayin haraji ga gidajen mutane su rika biya.
Mazauna wasu kauyukan jihar sun koka cewa haka kowa ke fama da matsalar ‘yan bindiga a yankin.
Discussion about this post