Kungiya mai zaman kanta mai suna ‘SING Nigeria’ ta bayyana cewa tsarin mulki na dimukuradiya zai yi zaman daram-dam ya ɗau saiti a Najeriya ne idan an daina cinikin kuri’un a wuraren zaɓe
Shugaban kungiyar Idris-Etanami Usman ya fadi haka a wata zama da kungiyar ta yin musayan ra’ayoyi kan zaɓen Anambra da aka yi ranar Asabar.
Usman ya ce lokaci ya yi da ƴan Najeriya za su rika haɗa mutane irin haka da hukuma domin a kawo karshen abin.
“Yanzu zabe a kasar nan ya zama kaman sana’a inda mutum zai zuba kudinsa sannan ya zauna ya jira riba. Dalilin hakan ya sa Ƴan siyasa ke yi ko ta halin ƙaƙa sun yi nasara a zaɓe.
“Ya kamata mutane su rika kai ‘yan siyasa kara a kotu idan wani ya bijiro musu da maganan cinikin kuri’ar su a lokacin zaɓe.
Bayan haka jami’in kungiyar Mohammed Basah ya yi kira ga shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya taimaka wajen ganin dokar inganta harkokin zabe ya fara aiki kafin zaben 2023.
“Muna kira ga hukumar zabe INEC da ta yi amfani da zaben da aka yi a jihar Anambra domin inganta aiyukkanta kafin zaben 2023.
“Muna kuma kira ga masu ruwa da tsaki a harkar zaɓen kasar nan kawo karshen siyan kuri’u a lokacin zaɓe a kasar nan.
Idan ba a manta ba a ranar Asabar din da ya gabata ne mutanen jihar Anambra suka fito da kwansu da kwarkwata domin zaben gwamnan jihar.
PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarai da bidiyo da dama kan yadda wakilan jam’iyoyi suka zo rumfunar da mutane ke jefa kuri’un su suna bai wa duk wanda ya jefa wa dan takaran su kudi.
Zuwa yanzu hukumar zabe INEC bayyana sakamakon zabe inda Charles Soludo na jami’iyyar APGA ya yi nasara a kananan hukumomi 18 cikin 21.
Discussion about this post