Gwamna Aminu Tambuwal ya tabbatar da cewa waɗanda ‘yan bindiga su ka kashe a mummunan harin baya-bayan nan a Illela da Goronyo sun kai mutum 45.
Tambuwal ya ce haka mutanen yankin su ka bayyana wa gwamnan a lokacin da ya kai ziyara a yankunan.
Wannan bayani na ƙunshe cikin takardar manema labarai da Kakakin Gwamna Tambuwal ya fitar wa manema labarai, ya ce a hare-haren waɗanda aka kai a ranakun Asabar da Lahadi, an kuma raunata mutane da dama, waɗanda yanzu haka dai ana yi masu magani a asibitin yankin.
Hare-haren su na ƙara muni ne, ganin cewa akwai alamomin farmakin ramuwar-gayya da ake kaiwa a yankunan.
Cikin watan Oktoba mahara sun kashe mutum 49 a cikin kasuwa. Kwanaki goma kafin nan kuma an kashe mutum 20 a Unguwar Lalle.
Buhari ya yi tir da kisan kiyashin da ake yi a Sokoto
Shugaban kasa Buhari ya yi tir da kisan kiyashin da ‘yan bindiga ke yi a jihar Sokoto.
Ya ce gwamnati baza ta bari wasu tsirarun ‘yan bindiga na kashe mutane haka kawai ba.
Shugaban kasa Buhari ya fadi haka ne a wati takarda da kakakinsa Garba Shehu ya fidda ranar Alhamis.
“Nan ba da dadewa ba maharan za su dandan kudan su a kasar nan.