A tarihin siyasar Najeriya, Jihar Anambra ce wadda aka fi nuna zunzurutu kuma tantagaryar jagaliyancin siyasa, domin a ci zaɓe da tsiya ko da tsinin tsiya.
A yanzu kuma Anambra na fama da rikicin ‘yan ƙungiyar IPOB waɗanda a baya suka sha alwashin hana a yi zaɓen.
Yayin da IPOB suka bada sanarwar amincewa a yi zaɓen, PREMIUM TIMES Hausa ta bi lamarin siyasa da matsalar tsaron jihar filla-filla, domin yin hasashen abubuwan da ka iya faruwa a lokacin zaɓe da kuma bayan zaɓen na Gwamnan Jihar Anambra, wanda za a yi ranar Asabar, 6 Ga Nuwamba.
1. Rikita-rikita Da Dambarwar Siyasar ‘Yan Takara:
Manyan ‘yan takarar gwamna daga jam’iyyar APC, PDP da APGA duk sun samu nasarar tsayawa ne daga hukuncin kotu, ba da ƙuri’un da su ka ci zaɓen fidda-gwani ba.
Wannan ya rage wa zaɓen da ita kan ta dimokraɗiyyar jihar armashi. Musamman idan aka yi la’akari da yadda zargin toshe wa alƙalai baki suka baddala hukunci.
Idan an tuna, har Babban Jojin Najeriya ya yi tofin Allah-waddai da wasu hukunce-hukuncen da wasu kotuna suka yanke.
Hakan ya sa ake ganin ko an jefa ƙuri’a ma akwai yiwuwar sai an sake komawa kotu domin tabbatar da wanda ya yi nasara, saboda babu wanda zai yarda an kayar da shi salum-alum.
2. Andy Uba: Tasirin Uban Gada-gadar Siyasa A Zaɓen Gwamnan Anambra:
Andy Uba cikakken dindin buhun ɗan jagakiyar siyasa ne. Idan ba a manta ba, cikin 2007 ya yi amfani da Hukumar Zaɓe aka ce ya yi nasarar zaɓen gwamna. Duk kuwa da cewa haramtaccen zaɓe ne. Sai da ta kai Kotun Ƙoli ta soke zaɓen shi, bisa dalilin cewa wa’adin mulkin gwamnan lokacin, Chris Ngige bai ƙare ba aka yi zaɓen.
Sannan kuma a lokacin ne dai idan ba a manta ba, yayan Andy Uba mai suna Chris Uba, ya yi amfani da ‘yan sanda 300 ya sace Gwamna Ngige na Jihar Anambra, tare da saye kakaf ɗin ‘yan majalisar jiha, suka tsige gwamnan. Duk da dai a ƙarshe haƙar su ba ta cimma ruwa ba.
A yau kuma gogarman jagaliya Andy Ubs ne ya fice daga PDP, ya tsaya takarar gwamnan a APC. Kuma alamomi sun nuna cewa ya fi sauran ‘yan takara ƙarfi sosai. Ga ƙarfin rigima, ga ƙarfin kuɗi, kuma ga ƙarfin gwamnatin APC duk a tare da shi.
Saboda haka ana hasashen cewa ko an kayar da Andy Uba, ba haƙura zai yi ba. Sannan kuma zai yi duk iyakar ƙoƙarin sa wajen ganin ko ana ha-maza-ha-mata ya yi nasara.
3. Matsalar Tsaro: Duk da cewa IPOB sun janye barazanar hana jama’a fitowa su yi zaɓe, har yanzu ana zaman ɗar-ɗar a manyan garuruwan jihar, musamman a Awka, babban birnin jihar, inda har yau Juma’a rahotanni su ka tabbatar cewa jama’a ba su fito waje sosai ba, saboda fargaba.
Idan aka wayi gari a irin wannan yanayi, za a samu ƙarancin masu jefa ƙuri’a kenan a ranar Asabar.
4. Dandazon Jami’an Tsaro A Birni Ba Ƙauyuka Ba:
Irin yadda aka danna dandazon Jami’an Tsaro a Jihar Anambra, ya taimaka wajen ganin cewa IPOB ta ji maganar manyan yankin, har ƙungiyar ta janye barazanar hana fita a jefa ƙuri’a ta yi a baya.
To amma mutane da dama na ganin ko da jami’an tsaro sun yi tasiri a cikin birane da garuruwa, to rashin su a wadace cikin yankunan karkara zai iya rage wa zaɓen armashi.
Kuma a yankunan karkara ake tunanin can masu tayar da zaune-tsaye za su fi cin karen su babu babbaka.
5. INEC: Duk Da Hukumar Zaɓe Ta Ce Ta Kimtsa, Tabbatar Da Sahihancin Zaɓe Sai An Kammala Tukunna:
Hukumar Zaɓe ta Ƙasa na ta shalar cewa ta yi shiri tsaf domin magance maguɗi, kuma an shirya kare lafiyar jami’an zaɓe manya da ƙanana.
Sai dai kuma akwai fargabar cewa gogaggun ‘yan takara za su iya shirya maguɗi a wasu sassan da jami’an tsaro ba su wadata ba, ko kuma mazaɓun da aka samu ƙarancin masu jefa ƙuri’a.
6. Masu Jefa Ƙuri’a: Ina Amfanin Baɗi Ba Rai?:
Yadda ‘yan takifen IPOB su ka rikita yankin Kudu maso Gabas, su na kisan jami’an tsaro da tarwatsa kadarorin gwamnati, da kai wa kayan INEC farmakin cinna wa kayan INEC wuta, wannan zai sa jama’a da dama su ji tsoron fita zaɓe domin su jefa ƙuri’a a ranar Asabar.
7. Nasara Ko Matsalar Zaɓen Gwamnan Anambra Manuniya Ce Ga Yadda Zaɓen 2023 Zai Kasance:
Ba sau ɗaya ko sau biyu ba, Shugaban Hukumar Zaɓe Farfesa Mahmood Yakubu ya sha cewa shi ya fi fargabar zaɓen da ba na ƙasa baki ɗaya ba, fiye da zaɓen ƙasa baki ɗaya.
“Saboda shi zaɓen da ba na ƙasa ba, gaba ɗaya ƙasar nan kowa shi zai zira wa ido. Kuma manyan ‘yan siyasa da masu mulki za su je jihar da ake wannan zaɓe su yi kane-kane.
“Amma a ranar zaɓen bai-ɗaya, kowa jihar sa zai nufa, ba shi ma da sukunin tambayar abin da ke faruwa a cikin wata jihar. Saboda a ranar kowa tasa ta fisshe shi kawai ya ke yi.
8. Ko Yarjejeniyar Da ‘Yan Takara Suka Cimma Za Ta Yi Tasiri A Lokacin Zaɓe?:
Dukkan ‘yan takara 18 daga jam’iyyu daban-daban sun rattaba hannu a kan yarjejeniyar a yi zaɓe lafiya, a kauce wa tashin hankali kuma kada magoya baya su hargitsa zaɓe.
An tattaɓa wannan yarjejeniya a gaban Tsohon Shugaban Ƙasa na Mulkin Soja, Abdulsalami Abubakar da kuma Babban Limamin Coci Bishof Hassan Kuka.
To sai dai kuma an sha rattaba irin wannan yarjejeniya a tsakanin ‘yan takara, amma kuma sau da yawa yarjejeniyar ba ta haifar da ɗa mai ido. Kuma ba ta hana a yi rikice-rikice da tashe-tashen hankula a sassa daban-daban da ake jefa ƙuri’a.
9. Satar Akwati, Rinton Ƙuri’u Da Fasa Taron Masu Zaɓe:
Waɗannan muggan laifuka ne da ake aikatawa a lokacin zaɓe, ko kuma a lokacin ƙidayar ƙuri’u. Sau da yawa kuma don an zuba dandazon ‘yan sanda, ba su da yawan da za su iya magance wannan salon maguɗin zaɓe.
Don haka ana ganin jihar Anambra za ta yi tasiri a zaɓen ranar Asabar, inda za a ga shin maguɗin zaɓe zai yi tasiri, ko ba za ya yi tasiri ba?
10. Da Wahala A Samu Cikowar Kungiyoyin Sa-ido Matsalar Tsaro:
Ko an samu cinkoson waɗannan ƙungiyoyin, sai dai kawai a wuraren da ake da cikakken tsaro sosai.