Daraktan Yaɗa Labarai na Rundunar Sojojin Najeriya, Onyema Nwachukwu ya nesanta mahukuntan tsaron Najeriya daga wani bayani da aka danganta da shi cewa, “Hedikwatar Tsaro ta gargaɗi sojojin Najeriya kada su kuskura su kifar da Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.”
Burgediya Janar Nwachukwu ya bayyana haka a ranar Asabar, inda ya ce labarin mai cike da ƙarairayi ya ruwaito wai “Hedikwatar tsaro ta ƙaryata ta yi tir da kiraye-kirayen da ake yi ga sojoji su ƙwace mulki.”
Ya ce jaridar yanar gizon da ta buga labarin ta buga ƙarya da ƙirƙirar labarin bogi ga “Kakakin Sojojin Najeriya.”
Ya ce abin da kawai ya sa wannan ƙirƙirarren labari ya ja hankali, shi ne saboda an alaƙanta labarin wai daga Daraktan Hulɗa da Jama’a na Sojojin Najeriya, Burgediya Janar Onyema Nwachukwu.
“Waɗanda suka kirƙiri wannan ƙarya su kaɗai ne gidan jaridar da ba su san cewa ba kowane Kakakin Soja ne ke magana da yawun Hedikwatar Tsaro ba.
“Amma duk da haka muna so mu warware wa jama’a zare da abawa cewa babu inda Daraktan Yaɗa Labaran Sojoji ya yi wannan kalami ko wani furuci makamancin haka.
“Kawai ƙarya ce da labarin bogi wasu su ka ƙirƙira, wadda kuma ba daga haki ko hannun Nwachukwu ta fito ba.”
Nwachukwu ya ce Sojojin Najeriya ba su buƙatar “a gargaɗe su kada su yi juyin mulki, domin sun sadaukar da biyayyar su ga Tsarin Mulkin Tarayyar Nigeria. Kuma biyayyar su na nan 100 bisa 100 ga Shugaban Najeriya kuma Babban Kwamandan Askarawan Najeriya.”
Discussion about this post