Wasu alƙaluman bincike da ƙungiyar Transparency International ta buga, ya nuna cewa hankalin ‘yan Najeriya ya karkata wajen ɗora laifin yawan cin rashawa a zamanin mulkin Olusegun Obasanjo, fiye da munin rashawa a zamanin mulkin marigayi Umaru ‘Yar’Adua, Goodluck Jonathan da kuma Shugaba Muhammadu Buhari.
Yayin da Obasanjo ya shafe shekaru takwas kan mulki, daga 1999 zuwa 2007, Yar’Adua ya yi shekaru uku, daga 2007 zuwa 2010. Shi kuma Jonathan ya shafe shekaru biyar, daga 2010 zuwa 2015.
Shugaba Buhari ke kan mulki a yanzu, inda ya shafe shekaru shida daga 2015 har zuwa yau 2021. Kuma sai cikin 2023 zai kammala wa’adin sa na biyu.
Geji Da Malejin Munin Rashawa Daga 1999 zuwa 2021:
Geji da Malejin Munin Rashawa, wato ‘Curruption Perception Index’ (CPI), wanda PREMIUM TIMES ta yi nazari daga 1999 zuwa yau, ya nuna cewa ‘yan Najeriya sun fi ganin an fi cin rashawa a zamanin mulkin Olusegun, 1999 zuwa 2007 da kashi 16.
Wani tunanin na su kuma ya nuna Najeriya na kan mizanin kashi 25 a zamanin marigayi Umaru ‘Yar’Adua, yayin da a zamanin Goodluck Jonathan kuwa, mizanin ya na kan kashi 25.8 ne.
Mulkin Shugaba Buhari a ƙididdigar 2015 zuwa 2020, an ɗora Najeriya a kan ma’aunin mizanin kashi 26.6.
Don haka tunanin ‘yan Najeriya na ƙaruwa ne daga wannan gwamnati zuwa waccan.
A cikin shekaru 20 dai mizanin awon munin cin rashawa a Najeriya ya riƙa cillawa sama, ko ya juya zuwa ƙasa, tsakanin matakin ta 90 zuwa ta 149 duk shekara.
A wannan awon mizani, ana amfani da 0 zuwa 100. Mai lamba 0 na nufin ita ce ƙasar da ta fi munin rashawa. Mai lamba 100 kuma ƙasar da ake mulki tsakani da gaskiya da bin ƙa’idar dokokin sarrafa kuɗaɗen ƙasa.
Tsakanin 1999 zuwa 2011, an yi amfani da 0 zuwa 10 aka ɗora ƙasashe kan sikeli. Amma a cikin 2012, sai ƙungiyar Transparency International (TI) ta canja malejin awon sikelin daga 0 zuwa 10, ta maida shi 0 zuwa 100.
Tun daga 2012, a shekarar 2016 ce Najeriya ta fi samun maki mai yawa, har kashi 28. Saɓanin zamanin Obasanjo da ta samu 16 kacal, zamanin ‘Yar’Adua maki 25, sai zamanin Jonathan maki 25.8.
S shekarar 2012, Najeriya ce ta 136 daga cikin ƙasashe 176 na duniya.
Amma a cikin 2002 zamanin mulkin Obasanjo, Najeriya ta zo ta 90 a cikin ƙasashe 91, inda ta samu maki 10 kacal.
A shekarar Shugaba Buhari ta biyu, wato cikin 2016, Najeriya ta samu maki 26.6. a cikin shekaru biyar na mulkin Buhari kuma, Najeriya ta riƙa samun daga maki 25 zuwa 28. Ta riƙa kasancewa a sahun ƙasahen da su ka fi tsantsenin rashawa da cin hanci sakamakon yaƙi da cin rashawar da Gwamnatin Buhari ke yi. Najeriya ta riƙa tsayawa a tsakanin lamba ta 136 zuwa ta 149, kamar yadda ƙididdigar ‘Transparency International’ ta tabbatar.
Sai dai kuma lamarin a Najeriya ya riƙa tafiyar maida hannun agogo baya, inda maimakon gejin rashawa ya riƙa raguwa, yadda Najeriya za ta riƙa samun ƙarin maki, sai abin ya riƙa ƙara muni.
Cikin 2017 maleji ya koma 27, haka a cikin 2018. Amma a cikin 2019 ya sauka zuwa 26. A 2020 kuma zuwa kashi 25.
Tsakanin 2016 zuwa 2020, Najeriya ta kasance tsakanin ta 136 a 2016, zuwa ta 149 cikin 2020.
Jadawalin mizanin dai ya tashi daga ta 1 zuwa 180. Ta 180 ita ce mafi munin hasashen cin rashawa.
Discussion about this post