Da farko dai, kalmar “feminism” ta samo asali ne daga kalmar “female ko femella” a yaren Girka, wanda take nufin yarinya, ko kuma mace.
Ma’anar ‘feminism’ shine aƙida, ko ra’ayin kare haƙƙin mata; ko kuma ƙoƙarin samar da daidaito tsakanin mata da maza – a fannin iko da haƙƙoƙin rayuwa.
An fara amfani da kalmar ‘feminism’ ne a shekarar 1840 bayan da aka ƙara wa kalmar ‘fēmina’ dafin “ism” – wanda yasa ya koma daukar ma’anar ra’ayi ko kuma aƙida. Amma a tarihi, mata sun fara nuna rashin goyon bayan su akan ikon da maza suke dashi akan su a shekarar 1840.
Sabida haka, aƙidar neman daidaita maza da mata ta ‘feminism’ tana nufin yin gwagwarmaya a fannin rayuwa, ko siyasa, ko tattalin arziki, ko kuma samar da daidaito tsakanin jinsi – wanda Zai bayar da damar yin raba dai-dai na haƙƙoƙi tsakanin namiji da mace.
Shi kuma tsarin aƙidar ‘feminism’ tana da shika-shikai har guda uku, wadanda suka hadar da nema wa mata yancin kai a fannin al’adu; da dabi’u da kuma tsarin rayuwa.
Daga cikin manufofin ‘feminism’ akwai yaƙi da bambancin dake tsakanin mata da maza, amma a cewar masu ra’ayin, ‘feminism’ ba ya nufin ƙasƙantar da jinsin maza.
Masana suna fadin cewa da yawa daga cikin masu aƙidar ‘feminism’ ba wai suna ƙin jinin aure bane; a’a sai dai suna ganin idan anyi auren, dole ne namiji ya baiwa mace na ta ikon; suyi raba dai-dai wajen cin-gashin kai.
A tsakanin ƙarni na 14 zuwa 15 wata masaniyar ilimin Falsafa ‘yar asalin ƙasar Faransa mai suna Christine de Pisan, ta fara ƙalubalantar yadda ake mu’amalantar mata, harma tayi kukan Kura; ta fara neman a baiwa mata damar neman ilimi.
Christine dai tana daga cikin matan da suke da ra’ayin cewa barin mata a ƙarƙashin maza; suna fin su iko a sha’anin mulki da ilimi ba – wanda take ganin yin hakan zai iya dawwamar da jinsin matan a baƙin talauci, da ƙasƙanci, da dawwama a matsayin ababen sha’awar maza da sauran su – abinda a turance suke yiwa laƙabi da ‘patriarchy’ ma’ana baiwa maza ikon tafiyar da al’amuran gida.
A aƙidar mafi yawan masu gwagwarmayar ‘feminism’ sun tafi akan cewa aure kamar bautar da jinsin mata ne, sabida ikon da maza suke dashi akan mata – sabida haka ba wajabta ba ga mace, yarinya, ta amince wa wani namiji ya aure ta har sai ya yarda zai yi watsi da duk wadansu tsarabe-tsaraben aure.
Wannan a ƙasar Hausa yanzu, wadansu daga cikin masu aƙidar ta ‘feminism’ suke nufi da mazajen su, su cigaba da sakar masu mara, suyi gwagwarmayar su da sauran mu’amalar su ba bu kwaba; ko kuma su riƙa daukar cewa akwai wadansu ayyukan gida wadanda ba dole ne su yiwa mazajen su ba – kamar girki, ko shara, ko wanki da sauran su.
Amma wannan ba ya hana mata masu wannan aƙidar su baiwa wani namijin zuciyar su, duk da irin tsauri, da wahalar soyayyar da suke da ita. Sabida mafi yawan lokuta idan namiji yana soyayya da Mai aƙidar ‘feminism’ suna yawan samun sabani na ra’ayi da fahimta da sauran su – wanda riƙar su a ciki kan janyo duk wanda yazo neman auren su, ba sa kaiwa ga matakin yin aure ake raba gari.
Su matan da suke da ra’ayi ko aƙidar ‘feminism’ sun fi so idan namiji yana soyayya dasu, ya daina nuna mata cewa yana da wata daraja sama da ita; sa’annan kada ya nuna mata yana sama da ita a shugabanci; sun fi so namiji wanda zai kwantar da kan sa ya koyi tsare-tsaren su; sa’annan ya zama mai saukin kai; ya zama mai ba su damarmakin su; ya zama mai gwagwarmaya da kuma ƙoƙarin samar wa mata damarmaki.
Akwai wadanda suke ganin cewa ana samu daga cikin mazaje da suke da aƙidar ‘feminism’ harma suke yin amfani da hakan wajen gorantawa sashin mazajen da suke sukar ra’ayin su, sukan cewa “ai a maza ma akwai wadanda muke yin harkar nan tare”.
Amma a shekarar 2001, an gano cewa kaso 20 cikin 109 na mazajen ƙasar Amurka suna da’awar aƙidar ‘feminism’ duk da cewa kashi 75 cikin 100 daga cikin su suna musanta hakan. Haka nan jaridar CBS a shekarar 2005 ta wallafa cewa kaso 24 cikin 100 na mazajen ƙasar Amurka suna ala-wadai da aƙidar ‘feminism’ harma sukan daukar ta a matsayin cin fuska.
Manyan ma su da’awar aƙidar ‘feminism’ a Duniya sun hadar da:
1. Hélène Cixous
2. Simone De Beauvoir
3. Naomi Wolfe
4. Germaine Greer
5. Doris Lessing
5. Andrea Dworkin
6. Malala Yousafzai da sauran su.