Ministan Shari’a Abubakar Malami, ya shaida wa Gwamnoni 36 na Najeriya cewa alƙalami ya bushe, tilas sai sun biya ‘yan gada-gadar kwangila dala miliyan 418 ɗin da hukuncin kotu ya gindaya masu.
Malami ya ce saboda haka gwamnatin tarayya ba za ta fasa fara cire dala miliyan 418 a hankali ba ta na dannawa asusun ‘yan gidogar, domin kotu ce ta yanke hukuncin cewa a biya su kuɗaɗen.
Kakkausan kalaman Malami sun zo ne mako ɗaya bayan da wata Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta tsaida fara cirar kuɗin daga asusun gwamnoni a riƙa biyan ‘yan kwangilar.
Su dai waɗannan ‘yan gidoga sun kai gwamnonin jihohi 36 ƙara, inda su ka nemi a biya su kuɗaɗen aikin tuntuɓa da su ka ce sun yi wa gwamnonin jihar, tsakanin 1995 da shekarun 2000, su ka taimaka domin a maida wa jihohin kuɗaɗen biyan bashin Paris Club da aka riƙa ɗibar masu fiye da ƙa’ida.
Sun kuma yi iƙirarin cewa sun yi aikin kwangiloli a jihohi 774 tun a wancan lokacin, amma ba a biya su ba.
Yayin da gwamnoni ke tababar ayyukan ‘yan gidoga, su ma shugabannin ƙananan hukumomin Najeriya sun ce a su ga wani aikin da ‘yan kwangilar su ka ce sun yi ba.
A yanzu da Ministan Shari’a Malami ya haƙikice sai an biya kuɗin, PREMIUM TIMES HAUSA ta sake bijiro masu da wannan kwatagwangwa kamar haka:
Hukuncin Da Malami Zai Yi Fatali Da Shi:
Kotu Ta Hana Kwasar Dala Miliyan 418 Daga Kuɗaɗen Gwamnoni A Biya Dillalan Gada-gada:
A ranar Juma’a ce Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta dakatar da Gwamnatin Tarayya kwasar dala miliyan 418 daga asusun jihohi 36 da ƙananan hukumomi 774, da nufin ta biya wasu dillalan gada-gada masu iƙirarin cewa sun yi wa jihohi da ƙananan hukumomi ayyukan adadin kuɗaɗen a shekarun baya.
Dillalan gada-gadar sun ce sun yi wa jihohi da ƙananan hukumomi aikin tuntuɓa ne da wasu kwangiloli tsakanin 1995 da 2002, wajen ƙoƙarin aikin dawo masu da kuɗaɗen da aka riƙa ɗibar masu ana biyan bashin Paris Club da London Club.
Babban Mai Shari’a Iyang Ekwo ya umarci Gwamnatin Tarayya ta dakatar da fara kwasar kuɗaɗen da ta shirya fara kwasa daga watan Nuwamba, har sai bayan an kammala shari’ar da Gwamnonin Najeriya 36 suka shigar a gaban sa.
Gwamnonin 36 sun shigar da ƙarar ta hannun gogaggun lauyoyin su biyu, Jibrin Okutedo da Ahmed Raji, waɗanda dukkanin su manyan lauyoyi ne (SAN).
A ƙarar da su ka shigar, lauyoyin sun shaida wa kotun cewa Gwamnoni 36 na Najeriya ba su yarda cewa waɗancan dillalan gada-gadar sun yi ayyukan da su ka ce sun yi a jihohi 36 da ƙananan hukumomi 774 a shekarun baya ba.
Lauyoyin sun ce masu iƙirarin sai an biya su haƙƙin kuɗaɗen har dala miliyan 418, ‘yan gidoga ne kawai, lamarin babu gaskiya a ciki.
“Kuma idan Gwamnatin Tarayya ta kwashi kuɗaɗe a asusun jihohi 36, to jihohin za su kasance a talauce, ta yadda biyan albashi ma ba zai yiwu ba.”
Daga cikin waɗanda gwamnoni 36 su ka kai ƙara, har da Ma’aikatar Harkokin Kuɗaɗe ta Tarayya, Ma’aikatar Harkokin Shari’a da Antoni Janar, kuma Ministan Shari’a da kuma Ofishin Bin-diddigin Kuɗaɗen Bashi (DMO) da kuma Kwamitin Rabon Kuɗaɗen Kasa na Gwmnatin Tarayya, wato FAAC.