Sakamakon zaɓen gwamnan Jihar Anambra da aka kaɗa a yau Asabar ya nuna cewa jama’a ba su fito sosai ba.
Sakamakon zaɓen rumfar da Andy Uba ya yi zaɓe ya tabbatar da adadin waɗanda su ka yi zaɓe ba su kai 150 ba kwata-kwata.
Daga ciki ƙuri’un da aka jefa, Andy Uba na APC ya yi nasara da ƙuri’u 80. Jam’iyyar APGA mai mulki ke bin APC da ƙuri’a 10, sai PDP kuma da ta samu ƙuri’a 2 kacal.
Akwai wasu jam’iyyu da su ka samu ƙuri’un da ba su kai uku ko huɗu-huɗu ba.
Andy Uba shi ne ɗan takarar APC. A zaɓen 2007 ya tsaya takara ne a ƙarƙashin PDP. Kafin lokacin kuma ya riƙe muƙamin Babban Hadimin tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo a ɓangaren harkokin cikin gidan Obasanjo.
Ya daɗe ya na neman zama gwamna a jihar Anambra, sai dai ana ganin komawar sa APC a zaɓen 2021, alama ce ta neman yin nasara da ƙarfin gwamnati mai mulki.
Sakamakon da ke fitowa ko shakka babu zai rage wa zaɓen armashi.
Bisa dukkan alamu wankin hula ya kai INEC dare, domin hukumar ta ƙara lokacin daina zaɓe zuwa ƙarfe 4 na yamma, zai yiwu a jefa ƙuri’a ranar Lahadi a wasu wuraren da aka samu tsaikon tantancewa.
Hukumar Zaɓe ta Ƙasa ta bayyana kai lokacin daina zaɓe a ranar Asabar zuwa ƙarfe 4 na yamma.
Hakan ya faru ne saboda tsaiko da jinkirin da aka samu wajen isar kayan zaɓe da jami’an zaɓe a wasu yankuna da wuri.
Haka kuma INEC ta bayyana cewa akwai yiwuwar a yi zaɓe a washegari Lahadi, a mazaɓun da aka samu mishkila wajen tantance masu jefa ƙuri’a.
Ɗan takarar jam’iyyar APGA Charles Soludo, ya nuna rashin jin daɗin yadda na’urorin tantance masu jefa ƙuri’a suka ƙi yin aiki ƙiri-da-muzu a lokacin tantance masu zaɓe.
Tuni dai har an fara ƙirga ƙuri’u a wuraren da aka kammala zaɓuka.
Discussion about this post