Shugaban Ƙaramar Hukumar Ijebu ta Gabas a Jihar Ogun ya surfa wa Gwamnatin Jiha tsinuwa da zagi, sakamakon ruguge matsugunan talakawa da aka yi a ƙaramar hukumar sa, sannan kuma aka banka masu wuta.
Wale Adebayo ya bayyana abin da aka yi wa talakawan da cewa, “an wulaƙanta su, an banka wa kayan su wuta kuma aka ruguza matsugunan su.”
A ranar Alhamis ce Adebayo ya shiga shafin sa na Facebook ya yi kakkausan rubutun da ya ragargaji gwamnatin jihar, tare da nuna cewa babu tausayin takakawa a zuciyar gwamnatin gaba ɗaya, saboda ta rushe matsugunan talakawa waɗanda ba su da muhalli, babu abincin yau ballantana na gobe.”
An dai gudanar da rusau ɗin da ƙone matsugunan talakawa marasa galihu da ke zaune a cikin Dajin Gwamnati.
Shugaban Ƙaramar Hukumar Ijebu ta Gabas inda aka yi rusau ɗin ba da sanin sa ba, ya ɗora laifin kan Ma’aikatar Kula da Gandun Dazuka ta Jihar Ogun, a ƙarƙashin Kwamishina Tunji Akinosi.
“Wannan rusau da gwamnati ta yi haramtacce ne, ya karya ƙa’ida, rashin tausayi ne ƙarara, kuma an cuci talakawan yanki na.”
Adebayo bai haƙura ba, sai da ya antaya tsinuwa da mummunar addu’a a kan duk wanda ke da hannu wajen abin da ya kira ƙuntata wa talakawan sa.
“Allah ya ɗora wa ‘ya’yan ku irin ƙuncin rayuwar da ku ka jefa talakawa a ciki.
“Ku ma wata rana sai kun zama abin tausayi kamar yadda ku ka maida talakawa abin tausayi.” Inji Adebayo, Shugaban Ƙaramar Hukumar Ijebu ta Gabas.
Sai dai kuma Kwamishinan Harkokin Gandun Daji Tunji Akinosi ya ce ba a yankin Ƙaramar Hukumar Ijebu ta Gabas ne aka fara yin wannan rusau ba.
“An yi a shiyyar J1 da Shiyyar J2. Sannan aka gangaro a shiyyar J3 cikin yankin sa. Kuma duk matsugunan da aka ruguza, ‘yan share-wuri-zauna ne su ka kafa su ba tare da izni ba.”
Kwamishinan ya ce kamata ya yi shugaban ƙaramar hukumar ya tuntubi ma’aikatar sa kafin ya fito ya na zarge-zarge.
Sai dai kuma Adebayo ya ce sai da tuntuɓi Babban Sakataren Ma’aikatar Kula da Gandun Daji tukunna.
Shugaban Ƙaramar Hukumar Ijebu ta Gabas dai shi ma ɗan jam’iyyar APC ne, wadda Gwamna Dapo Abiodun na jihar ke ciki.