Sabuwar rikici ta kicime a Jam’iyyar APCn Karamar Hukumar Fagge dake a Jihar Kano tsakanin Dan Majalissar Tarayya mai wakiltar mazabar ta Fagge a Abuja Aminu Goro, da ciyaman na Karamar Hukumar Fagge, Abdullahi Shehi.
Shugaban na Karamar Hukumar Fagge, cikin wani bidiyo daya saka, ya zargi Dan Majalisar Tarayya Aminu Goro da shirya masa manakisa wajen bincikar da Hukumar da’ar ma’aikata (Code of Conduct Bureau) take yi masa akan zargin almundahana da kudin harajin Karamar Hukumar Fagge.
Dukkaninsu dai ‘ya’yan Jam’iyyar APC ce mai mulki, amma kowanne da gidansa a Jam’iyyar.
Shehi yace ya samarwa matasa 287 aikin karbar haraji a Karamar Hukumar Fagge amma Aminu Goro yana masa bita da kulli akan hakan.
Sau 41 aka rubuta korafi (petition) akaina kuma na je Hukumar da’ar ma’aikata sau hudu a Abuja, yau ba’a fi kwana uku ba sai da aka yi beli na, kuma Suleiman Goro shi yake hada wannan manakisar, inji shugaban na Karamar Hukumar.
Shehi yace lokacin da ya hau mulki, ya tarar dokar haraji ta bada dama ga ma’aikata masu karbar haraji su dauki kashi uku zuwa hudu na abinda aka tara, amma muka sabonta dokar muka mayar dashi cewa a baiwa ma’aikatar kashi ashirin na harajin da aka tara domin taimakawa da samun inganci.
Ya zama wajabi mu gayawa mutanen Fagge su san abinda ake ciki, inji Shehi
Goro ya musanta zargin Shehi
Aminu Goro ya musanta dukkanin zargin da Shehi yayi masa, kuma ya sha alwashin zuwa kotu domin bata masa suna da shugaban na Karamar Hukumar yayi.
Goro yace a cikin shekaru hudu da Shehi yayi babu wani aikin cigaban al’umma da yayi duk da cewa Karamar Hukumar Fagge tafi kowanne Karamar Hukumar a Kano tara kudin haraji.
Shi Shehi ya kirkiri wannan magana domin ya janye hankalin mutanen Fagge kan gazawarsa shi da iyayen gidansa na kasa aiwatar da komai cikin shekaru hudu da yayi yana mulkin Karamar Hukumar Fagge.
Babu wane aiki na cigaban al’umma na N10 million da sukayi, ko titi, ko magudanan ruwa, ko makaranta a Karamar Hukumar Fagge duk da miliyoyin nairori da suke tarawa daga haraji, inji Goro.
Muna nan muna shirya lauyoyin mu domin garzaya kotu a bi mana hakkin mu akan bata min suna da yayi.
Discussion about this post