An bada sanarwar rasuwar Sani Ɗangote a ranar Lahadi, wanda ƙani ne ga Aliko Ɗangote.
Sani, wanda shi ne Mataimakin Shugaban Rukunin Kamfanonin Ɗangote Group, ya rasu a wani asibiti a ƙasar Amurka.
Ya rasu bayan wata rashin lafiyar da ba a bayyana irin ta ba.
Sani ba mutum ne mai yawan magana ba, ya na harkokin sarrafa kayayyaki, harkar noma, gine-gine, harkokin mai a duniya.
Shi ne Shugaban Hukumar Gudanarwar Dangote Suger, Dangote Cement, Ɗangote Agro Sacks, Ɗangote Refinery, Petrochemical and Fertilizer Company.
An fi sanin sa da kamfanin sa na Dansa, wanda wani ɓangare ne na Dangote Group, mai yin kayan lemukan marmari.
Shi ke da Dansa Food da Dangote Farms da sauran wasu kamfanoni.
Rasuwar Sani Ɗangote za ta girgiza Nageriya da wasu ƙasashe da dama, musamman ya rasu daidai lokacin da ake ƙoƙarin kammala aikin ginin katafariyar matatar mai ta Dangote Refinery a Legas, wadda duk Afrika babu irin ta.
Da wannan masana’anta ce Najeriya ta dogara domin samun sauƙin sayen tataccen man fetur da arha a Najeriya.