• PREMIUM TIMES |
  • Tallata Hajar ka |
  • Adireshin mu |
  • PTCIJ |
  • Dubawa
Premium Times Hausa
  • Labarai
    • All
    • Duniya
    Peter Obi ya fice daga PDP

    Peter Obi ya fice daga PDP

    TATTAUNAWA DA SARAKI:’Idan na zama shugaban ƙasa zan magance aringizon kuɗaɗen da ake yi wajen bayar da kwangiloli’

    TATTAUNAWA DA SARAKI:’Idan na zama shugaban ƙasa zan magance aringizon kuɗaɗen da ake yi wajen bayar da kwangiloli’

    Dino Melaye

    Dino Melaye ya sha ƙasa a zaben fidda gwani na jam’iyyar PDP a Kogi

    EFCC ta cafke Okorocha bayan mamaye gidan sa da jami’an tsaro suka yi tun 11 na safe

    EFCC ta cafke Okorocha bayan mamaye gidan sa da jami’an tsaro suka yi tun 11 na safe

    Dalilin da ya sa ƴan bindiga ke ci gaba da kai wa mutane hari a jihar Neja – SSG

    Yadda ƴan bindiga suka kashe mutum 11 a Zamfara a karshen makon jiya

    SHUGABAN ƘASA 2023: ‘Yan takarar APC na jihohin ƙabilar Igbo sun yi taron jiran-gawon-shanun goyon bayan duk wanda ya samu tikiti a cikin su

    SHUGABAN ƘASA 2023: ‘Yan takarar APC na jihohin ƙabilar Igbo sun yi taron jiran-gawon-shanun goyon bayan duk wanda ya samu tikiti a cikin su

    TAKARAR SHUGABAN KASA: Muna tare da kai a koda yaushe – Sarkin Katsina Abdulmumini ga Osinbajo

    TAKARAR SHUGABAN KASA: Muna tare da kai a koda yaushe – Sarkin Katsina Abdulmumini ga Osinbajo

    TA KICIME A APCn KADUNA: Ɓangaren Sha’aban ba su amince da zaben wakilan jam’iyyar APC da aka yi ba

    TA KICIME A APCn KADUNA: Ɓangaren Sha’aban ba su amince da zaben wakilan jam’iyyar APC da aka yi ba

    Yadda sojoji suka cafke gogarman masu garkuwa da mutane da wasu 150 a dazukan Zamfara da Katsina

    Askarawan Najeriya sun kashe ƴan bindiga 42, sun kama 20 sannan sun ceto mutum 63 da aka yi garkuwa da su – DHQ

  • Labarai daga Jihohi
  • Wasanni
    CHAMPIONS LEAGUE: Ko dai tsinuwar Yaya Toure ta yi tasiri kan Pep Guardiola?

    CHAMPIONS LEAGUE: Ko dai tsinuwar Yaya Toure ta yi tasiri kan Pep Guardiola?

    PILLARS SUN KIRA RUWA: Daga yanzu a Abuja za su rika wasan gida kuma an zaftare musu maki 3

    PILLARS SUN KIRA RUWA: Daga yanzu a Abuja za su rika wasan gida kuma an zaftare musu maki 3

    Yadda Kanawa suka yi ragaraga da motar ƴan  Katsina United saboda Pillars ta buga kunnen doki a Kano

    Yadda Kanawa suka yi ragaraga da motar ƴan Katsina United saboda Pillars ta buga kunnen doki a Kano

    GHANA vs NAJERIYA: Ko Najeriya za ta kauce wa ɗauko buhun kunya na 26 a hannun ‘Black Stars’?

    GHANA vs NAJERIYA: Ko Najeriya za ta kauce wa ɗauko buhun kunya na 26 a hannun ‘Black Stars’?

    Barcelona ta yi wa Madrid dukan kabarin kishiya, ba sani ba sabo ta zura mata kwallaye 4 babu ko ɗaya

    Barcelona ta yi wa Madrid dukan kabarin kishiya, ba sani ba sabo ta zura mata kwallaye 4 babu ko ɗaya

    ‘CHAMPIONS LEAGUE’: Yadda Benzama ya ceto Madrid daga rijiya gaba dubu, ya kori PSG kuma ya dawo da martabar sa a duniyar ƙwallo

    ‘CHAMPIONS LEAGUE’: Yadda Benzama ya ceto Madrid daga rijiya gaba dubu, ya kori PSG kuma ya dawo da martabar sa a duniyar ƙwallo

    YAƘIN UKRANIYA YA CI ƘUNGIYAR CHELSEA: ‘Zan sayar da kulob ɗin na sadaukar da kuɗin ga tallafin waɗanda yaƙin Ukraniya ya kassara’ -Abramovich, mai ƙungiyar kuma ɗan asalin Rasha

    YAƘIN UKRANIYA YA CI ƘUNGIYAR CHELSEA: ‘Zan sayar da kulob ɗin na sadaukar da kuɗin ga tallafin waɗanda yaƙin Ukraniya ya kassara’ -Abramovich, mai ƙungiyar kuma ɗan asalin Rasha

    RASHA: FIFA da UEFA sun dakatar da ƙungiyoyin Rasha buga wasannin ƙwallon Turai da duniya baki ɗaya

    RASHA: FIFA da UEFA sun dakatar da ƙungiyoyin Rasha buga wasannin ƙwallon Turai da duniya baki ɗaya

    KYAUTAR NAIRA MILIYAN 2: Allah ya saka wa Ahmed Musa, ina kira ga ‘yan wasa na yanzu su yi tattali don gaba – Obiekwue

    KYAUTAR NAIRA MILIYAN 2: Allah ya saka wa Ahmed Musa, ina kira ga ‘yan wasa na yanzu su yi tattali don gaba – Obiekwue

  • Kiwon Lafiya
  • Nishadi
  • Bidiyo da Hotuna
    KURUNKUS: Malami ya fito takarar gwamnan Kebbi, ya ce jama’ar jihar ne suka tilasta masa ya fito

    KURUNKUS: Malami ya fito takarar gwamnan Kebbi, ya ce jama’ar jihar ne suka tilasta masa ya fito

    2023: Ɗan takarar shugaban kasa, Rotimi Amaechi ya ziyarci masarautar Dutse

    2023: Ɗan takarar shugaban kasa, Rotimi Amaechi ya ziyarci masarautar Dutse

    LABARI CIKIN HOTUNA: Yadda ƴaƴan jam’iyyar APC da dubban mutanen Kaduna suka yi wa Sanata Uba Sani goma ta arziki

    LABARI CIKIN HOTUNA: Yadda ƴaƴan jam’iyyar APC da dubban mutanen Kaduna suka yi wa Sanata Uba Sani goma ta arziki

    BIDIYO: Shin zaka iya zama da mai dauke da cutar Kanjamau? – Ra’ayoyin mutane

    BIDIYO: Shin zaka iya zama da mai dauke da cutar Kanjamau? – Ra’ayoyin mutane

    Dalilin da ya sa muka yi tattaki har Dubai domin taya Aisha Buhari murnar zagayowar ranar haihuwar ta – Matan Gwamnonin Najeriya

    Dalilin da ya sa muka yi tattaki har Dubai domin taya Aisha Buhari murnar zagayowar ranar haihuwar ta – Matan Gwamnonin Najeriya

    BIDIYO: Yadda ‘yan bindiga suka rika jibga ta kafin a biya naira 50,000 kudin fansa – Dattijo Saidu Dabo

    BIDIYO: Yadda ‘yan bindiga suka rika jibga ta kafin a biya naira 50,000 kudin fansa – Dattijo Saidu Dabo

    ‘Yan mata marasa aure sun fi matan aure amfani da magungunan takaita Iyali – Ma’aikatar Lafiya

    ‘Yan mata marasa aure sun fi matan aure amfani da magungunan takaita Iyali – Ma’aikatar Lafiya

    BIDIYO: Kwalaben ruwan maganin rigakafin Korona sama da Miliyan daya da aka lalata a Abuja saboda sun gama aiki kafin a dirka wa ‘yan Najeriya

    BIDIYO: Kwalaben ruwan maganin rigakafin Korona sama da Miliyan daya da aka lalata a Abuja saboda sun gama aiki kafin a dirka wa ‘yan Najeriya

    BIDIYO: RIKICIN BILLIRI: Yadda muka rasa ‘yan uwa da dukiyoyin mu a rikicin sarauta – Galadiman Tangale

    BIDIYO: RIKICIN BILLIRI: Yadda muka rasa ‘yan uwa da dukiyoyin mu a rikicin sarauta – Galadiman Tangale

No Result
View All Result

Ra’ayoyi Da Fahimtar Malaman Musulunci Game Da Ranar Haihuwa Da Mutuwar Manzon Allah (SAW), Daga Imam Murtadha Gusau

Premium Times HausabyPremium Times Hausa
November 3, 2021
in Ra'ayi
0
Imam Murtada Gusau

Imam Murtada Gusau

Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jin Kai

Assalamu Alaikum

Ya ku al’ummar Musulmi, al’ummar Annabi Muhammad (SAW), kamar yadda kuka sani ne, an wayi gari yau Musulmi a duniya da kuma nan gida Najeriya, a koda yaushe, musamman idan watan Rabi’ul Awwal ya tsaya, suna tattauna wata mas’ala muhimmiya, wadda wani lokaci ta kan jawo hayaniya da cece-kuce, tare da batanci da cin mutuncin juna, kai har da yanke wa juna hukuncin cewa su ‘yan wuta ne, ko kuma kafirta juna, musamman idan wai sun yarda da cewa ranar 12 ga watan Rabi’ul Awwal, ita ce ranar da aka haifi Manzon Allah (SAW).

Abun tambaya game da wannan mas’ala shine, wai shin a wane wata ne da rana aka haifi Manzon Allah (SAW), kuma a wane wata ne da ranar da ya rasu.

Game da wannan muhimmiyar tambaya, mai cike da sarkakiya da rudani, ni dai abunda zan ce, kuma tare da fata da rokon Allah Subhanahu wa Ta’ala yayi man muwafaka, shine:

Da farko, ya kamata mu fahimci cewa, masana tarihi, na can da da na yanzu, sun yi sabani game da ainihin wata da kuma ranar haihuwar Manzon Allah (SAW). Wannan sabani na su abu ne dadadde, ba sabon al’amari bane. Don haka shi yasa ma wasu malamai suke ganin cewa, babu wata hujja mai karfi da ta ke tabbatar da cewa lallai ga ainihin rana, ko watan da aka haifi Manzon Allah (SAW). Wasu Malamai suka ce, abun da ya kawo haka kuwa shine, saboda a lokacin da aka haifi Manzon Allah (SAW), babu wanda yasan me zai zama a duniya, kuma babu wanda yasan matsayinsa, shi yasa ba’a mayar da hankali wurin sanin takamaiman rana da watan haihuwar sa ba (SAW).

Babban Malami, kuma masanin tarihi, Dakta Muhammad at-Tayyib an-Najjar (rahimahullah) ya fada, a cikin littafin sa mai albarka, mai suna, ‘AL-QAWLUL MUBIN FI SIRATI SAYYIDIL MURSALIN, shafi na 78, cewa:

“Hakika sanadiyyar abun da ya jawo wannan sabanin ra’ayin shine, saboda lokacin da aka haifi Manzon Allah (SAW), babu wanda yayi zato ko tsammanin cewa zai cimma wannan matsayi na rayuwa a cikin wannan al’ummah. Shi yasa ba wanda ya mayar da hankali gare shi a farkon rayuwar sa. Bayan Allah Madaukaki ya kaddari wannan Manzo na sa (SAW) ya isar da sakon sa zuwa ga bayin sa, bayan ya cika shekaru arba’in da haihuwa, sai mutane suka fara mayar da hankali gare shi, suka fara tattara dukkan wasu bayanai, da duk wani abu da suka sani game da rayuwar Annabi (SAW). Kuma sannan babban abun da ya taimaka masu a wannan muhimmin aiki shine, abun da shi kan sa Annabin (SAW) ya ba da labari na abun da ya sani game da abubuwan da suka faru a lokacin haihuwar sa, da kuma abubuwan da aka samu na bayanai daga wurin Sahabban sa, da sauran masanan da suke da masaniya game da abun da ya faru lokacin haihuwar ta sa (SAW). A wannan lokaci ne Musulmi suka fara tattarawa, tare da kokarin ajiye duk wani abun da suka ji na rayuwar sa, da nufin isar da shi ga wadanda za su biyo bayan su nan gaba.”

Na biyu, ya kamata mu sani, daga cikin al’amurran da Malamai suka yi ijma’i game da haihuwar Manzon Allah (SAW) shine, fassara rana da shekarar da aka haife shi (SAW):

1. Game da shekarar: Malamai suka ce ita ce shekarar giwaye. Ibn al-Qayyim (rahimahullah) yace:

“Babu sabani a wurin Malamai baki daya, cewa an haifi Manzon Allah (SAW) ne a garin Makkah, kuma a cikin shekarar giwaye.” [Duba Zadul Ma’ad fi Hadyi Khairil Ibad, mujalladi na 1, shafi na 76]

Kuma Sheikh Muhammad Ibn Yusuf as-Salihi (rahimahullah) yace:

“Ibn Is’haq (rahimahullah) yace: an haife shi ne a shekarar giwaye.”

Imam Ibn Kathir, shi ma yace:

“Abu ne sananne, wannan shine ra’ayin jumhur (wato mafi yawan Malamai), cewa an haife shi ne a shekarar giwaye.”

Sheikh Ibrahim Ibn Munzir al-Hizami, Babban Malamin Imamu Bukhari, yace:

“Wannan shine ra’ayin da babu wani malami da yake da shakku akai, cewa an haife shi ne (SAW) a shekarar giwaye. Khalifah Ibn Khayyat, Ibn al-Jazzar, Ibn Dihyah, Ibn al-Jawzi da Ibn al-Qayyim, duk sun tabbatar da cewa wannan ijma’i ne.” [Duba Subulul Huda war-Rashad fi Sirati Khairil Ibad, mujalladi na 1, shafi na 334 da 335]

Sannan Dakta Akram Diya’ al-Umari (rahimahullah) yace:

“A gaskiya, dukkanin ruwayoyin da suka nuna sabanin haihuwar sa (SAW) cikin shekarar giwaye, suna da matsala; akwai ruwayoyin da suka nuna an haife shi ne shekaru goma, ko ashirin, ko arba’in, bayan shekarar giwaye. Amma jumhur, wato mafi yawan Malaman Musulunci, sun tafi ne akan cewa an haife shi ne a shekarar giwaye. Kuma ko binciken da aka yi na kwanan nan, wanda Musulmi da ma wadanda ba Musulmi ba, masana masu bincike suka gabatar, sun tabbatar da hakan. Suka ce shekarar giwayen ma tayi daidai da shekarar 570 CE ko 571 CE.” [Duba As-Sirah an-Nabawiyyah as-Sahiha, mujalladi na 1, shafi na 97]

2. Game da ranar da aka haife shi (SAW):

Ranar da aka haife shi (SAW) ita ce litinin. An haife shi ne ranar litinin, Manzancinsa (wato wahayi) ya fara ne kuma a ranar litinin, kuma ya rasu ranar litinin.

An ruwaito daga Abu Qatadah al-Ansari (Allah ya yarda da shi), yace:

“An tambayi Manzon Allah (SAW) game da azumin da yake yi na ranar litinin, sai yace: “Ranar litinin ne aka haife ni, kuma ita ce ranar da aka fara yi mani wahayi.” [Muslim ne ya ruwaito shi]

Imam Ibn Kathir (rahimahullah) yace:

“Wadanda suka ce an haifi Manzon Allah (SAW) ranar Jumu’ah, 17 ga watan Rabi’ul Awwal, sun yi kuskure. Al-Hafiz Ibn Dihyah ya ba da labarin haka daga abun da ya karanta a cikin littafin Shi’ah, mai suna: I’ilamul wara bi A’alamul Huda. Ya bayar da labarin cewa wannan fahimta mai rauni ce, saboda ta saba wa nassi.” [Duba As-Sirah an-Nabawiyyah, mujalladi na 1, shafi na 199]

Na uku, game da bangaren da ake da sabanin Malamai sosai a cikin sa, shine watan da aka haife shi da kwanan watan. Akwai ra’ayoya da yawa, kamar haka:

1. Wasu Malamai sun ce an haife shi ne ranar biyu ga watan Rabi’ul Awwal.

Imam Ibn Kathir (rahimahullah), yace:

“Wasu Malamai sun ce an haife shi ne ranar biyu ga watan Rabi’ul Awwal. Ibn Abdul-Barr ne ya fadi haka a littafin sa mai albarka, wato al-Isti’ab, sannan kuma an ruwaito daga Imam al-Waqidi, daga Abu Ma’ashar Nujaih Ibn Abdur-Rahman al-Madani.” [Duba As-Sirah an-Nabawiyyah, mujalladi na 1, shafi na 199]

2. Wasu Malamai kuwa suka ce an haife shi ne ranar takwas ga watan Rabi’ul Awwal.

Imam Ibn Kathir (rahimahullah) yace:

“Wasu sun ce an haife shi ne ranar takwas ga watan Rabi’ul Awwal. An bayar da wannan labari ne daga Imam al-Humaidi daga Ibn Hazm, sannan kuma daga Malik, daga Aqil, Yunus Ibn Yazid da wasunsu, daga Imam az-Zuhri daga Muhammad Ibn Jubair Ibn Mut’im. Kuma Imam Ibn Abdul-Barr yace, Malaman tarihi sun tabbatar da ingancin hakan; kuma al-Hafizul Kabir, Imam Muhammad Ibn Musa al-Khawarizmi ya fadi haka, kuma Imam al-Hafiz Abul Khattan Ibn Dihyah yace wannan shine zancen da ake kallo a matsayin zama mafi inganci, a cikin littafin sa mai suna, at-Tanwir fi Mawlidil Bashirin-Nazir.” [Ka duba As-Sirah an-Nabawiyyah, mujalladi na 1, shafi na 199]

3. Wasu Malamai sun ce an haife shi ne ranar goma ga watan Rabi’ul Awwal.

Imam Ibn Kathir (rahimahullah), yace:

“Wasu sun ce an haife shi ne ranar goma ga watan Rabi’ul Awwal. Ibn Dihyah ne ya bayar da wannan labari a cikin littafin sa; haka Imam Ibn Asakir ya fadi haka daga Abu Ja’afar al-Baqir. Haka an ruwaito haka daga Mujahid daga ash-Sha’abi.” [Duba As-Sirah an-Nabawiyyah, mujalladi na 1, shafi na 199]

4. Wasu Malamai kuwa suka ce an haife shi ne ranar sha biyu ga watan Rabi’ul Awwal.

Imam Ibn Kathir (rahimahullah), yace:

“Wasu sun tafi akan an haife shi ne ranar sha biyu ga watan Rabi’ul Awwal. Imam Ibn Is’haq (rahimahullah), shine ya tabbatar da haka. Kuma Imam Ibn Abi Shaibah ya bayar da wannan labari a cikin littafin sa mai albarka, mai suna, ‘Musannaf’ daga Affan daga Sa’id Ibn Mina, cewa Jabir da Ibn Abbas sun ce: Manzon Allah (SAW) an haife shi ne a shekarar giwaye, ranar litinin, sha biyu ga watan Rabi’ul Awwal; ranar litinin ne ya fara karbar wahayi, ranar litinin ne aka yi Isra’i da Mi’raji da shi, yayi hijirah ranar litinin, sannan ya rasu ranar litinin. Kuma wannan shine ra’ayi mafi shahara kamar yadda mafi yawancin Malamai suka tafi akai. Kuma Allah shine mafi sani.” [Duba As-Sirah an-Nabawiyyah, mujalladi na 1, shafi na 199]

Ban da ma wadannan ra’ayoya, akwai ra’ayin wasu Malamai da ke cewa, an haife shi ne a cikin watan Ramadan ko watan Safar ko kuma wani watan.

Saboda haka, ya ku ‘yan uwa na Musulmi masu albarka, yanzu dai abun da ya bayyana a gare mu, a fili, karara, game da ainihin ranar da aka haifi Manzon Allah (SAW), bisa zance mafi inganci, sai in ce; game da ranar, tabbas Malamai sun yi sabani a kan hakikanin ta, amma dai sai duk mu yarda kuma mu amince cewa, ranar tana nan tsakanin takwas zuwa sha biyu (8-12) ga watan Rabi’ul Awwal. Wasu Malamai Musulmi masana ilimin lissafi da Malamai masana ilimin taurari ma sun tafi akan cewa ranar litinin da aka haifi Manzon Allah (SAW), ta fado ne daidai tara ga watan Rabi’ul Awwal, a bisa ingantaccen lissafi. Ana iya cewa wannan kuma wani ra’ayi ne na wasu Malaman, kuma tabbas shima akwai kanshin gaskiya a cikin sa. Kuma idan anyi lissafi, za’a ga cewa yayi daidai da 20th ga Afrilu 571 CE. Wannan kuma shine ra’ayin da mafi yawancin marubutan zamani game da rayuwar Manzon Allah (SAW) suka tafi a kai, cewa shine mafi inganci; kamar Farfesa Muhammad al-Khudari da kuma Sheikh Safi’ur Rahman al-Mubarakfuri.

Imam Abul Qasim as-Suhaili (rahimahullah), yace:

“Masana ilimin lissafi sun ce, an haife shi ne a cikin watan Afrilu, kuma ranar sha biyu ga watan afrilu din.” [Duba littafin Ar-Rawdul Unuf, mujalladi na 1, shafi na 282]

Farfesa Muhammad al-Khudari (rahimahullah) yace:

“Masanin ilimin taurarin nan, Dan kasar Misrah, wato Mahmoud Basha, wanda kwararre ne a fannin ilimin taurari da lissafi, yayi bincike, kuma ya rubuta littafai masu tarin yawa, yace: ranar litinin ne da safe, tara ga watan Rabi’ul Awwal, wanda yayi daidai da 20th Afrilu, 571 CE. Shekara daya bayan shekarar giwaye. Kuma an haife shi ne a gidan Abu Talib, a Shi’abu Banu Hashim.” [Duba littafin Nurul Yaqin fi Siratu Sayyidil Mursalin, shafi na 9, da kuma littafin ar-Rahiq al-Makhtum, shafi na 41]

Na hudu, shine game da kwanan watan da Manzon Allah (SAW) ya rasu. Lallai babu sabanin ra’ayi a wurin Malamai cewa, ranar litinin ne Annabi (SAW) ya rasu. Ra’ayin da aka ruwaito daga Ibn Qutaibah, da ke cewa ya rasu ne ranar laraba, baya da inganci. Malamai suka ce watakila abun da yake nufi shine an binne Manzon Allah (SAW) ranar laraba, wanda wannan kuwa gaskiya ne.

Game da shekarar rasuwarsa kuwa, babu sabani a wurin Malamai cewa ya rasu ne a shekara ta sha daya bayan hijirah (11 AH).

Game da watan da ya rasu kuwa, shima babu sabanin Malamai cewa ya rasu ne a cikin watan Rabi’ul Awwal.

Game da cewa nawa ne ga wata kuwa, akwai sabanin Malamai game da haka:

1. Jumhurun Malamai (wato mafi yawancin Malamai) sun tafi akan ya rasu ne ranar sha biyu ga Rabi’ul Awwal.

2. Imam al-Khawarizmi yana kan ra’ayin cewa ya rasu ne ranar daya ga Rabi’ul Awwal.

3. Imam Ibn Kalbi da Imam Abu Makhnaf suna da ra’ayin cewa ya rasu ne ranar biyu ga Rabi’ul Awwal. Imam as-Suhaili ya karkata ga goyon bayan wannan ra’ayi, kuma Imam al-Hafiz Ibn Hajar (rahimahullah) yana ganin cewa wannan shine ra’ayi mafi inganci.

Amma ra’ayi mafi shahara shine, wanda mafi yawancin Malamai suka tafi akai, cewa Annabi (SAW) ya rasu ne ranar sha biyu ga watan Rabi’ul Awwal, kuma a shekara ta sha daya bayan hijirah (11 AH). [A duba littafin ar-Rawdul Unuf, na Imam as-Suhaili, mujalladi na 4, shafi na 439 da 440; da As-Sirah an-Nabawiyyah, na Imam Ibn Kathir, mujalladi na 4, shafi na 509; da Fat-hul Bari na Imam al-Hafiz Ibn Hajar, mujalladi na 8, shafi na 130]

Allah shine mafi sani.

Don haka ya ‘yan uwa na al’ummar Annabi Muhammad (SAW), tun da dai har akwai maganganu da sabani da ra’ayoyan Malamai akan wannan mas’ala, to ina ganin sam bai dace a kafirta Musulmi, ko ace zai shiga wuta saboda wai yace shi ya yarda da cewa an haifi Manzon Allah (SAW) ne ranar sha biyu ga watan Rabi’ul Awwal. Idan an yi haka a gaskiya an tsananta, an zafafa kuma an wuce-gona-da-iri.

Kuma don Allah, don Allah, don Allah, a halin da al’ummah muke ciki yanzu, ba lokaci bane na hayaniya da fadace-fadace, da cin mutuncin juna a tsakanin al’ummah; ya kamata mu shiga taitayinmu. Jama’ah ko wannan kashe-kashe, da zubar da jinin bayin Allah, da sauran matsalolin rashin tsaro da kuncin rayuwa da suka addabi wannan al’ummah, wallahi sun isa su sa mu koma ga Allah, mu nemi gafararsa, mu hada kawunanmu, mu nemi mafita, ko Allah ya tausaya muna!

Ina rokon Allah Subhanahu wa Ta’ala ya shirye mu, yasa mu nisanci kafirta ‘yan uwan mu Musulmi, ko kuma kai su wuta, amin.

Nagode, nagode, nagode.

Dan uwan ku, Imam Murtadha Muhammad Gusau, daga Okene, Jihar Kogi, Najeriya. Za’a iya samun Imam a adireshi kamar haka: gusauimam@gmail.com, ko kuma wannan lambar: 08038289761.

Tags: 'Yan UwaAbujaLabaraiMusulmiNajeriyaNewsQutaibahSAW
Previous Post

HOTUNA: Gwamna Zulum ya sake buɗe titin Bama zuwa Banki

Next Post

Ganduje zai raba wa talakawan Kano akwatinan talabijin 100,000 kyauta

Next Post
ZABEN KANANAN HUKUMOMIN KANO: Sai an yi wa kowani Dantakara gwajin ko yana shaye-shaye – Umarnin Ganduje

Ganduje zai raba wa talakawan Kano akwatinan talabijin 100,000 kyauta

Binciko

No Result
View All Result
Karanta

Ramadan Kareem AD

Sabbin Labarai

  • SHIRIN CIYAR DA ƊALIBAI: Gwamnati za ta kashe naira miliyan 999 a kullum wajen ciyar da ‘yan makaranta miliyan 10
  • Isah Ashiru ya doke Ramalan Yero, Sani Sidi, ya zama ɗan takarar gwamnan Kaduna na PDP
  • Peter Obi ya fice daga PDP
  • Ba mu yadda mu janye wa mutum ɗaya ba, a shiga filin daga a fafata kawai – Ƴan takarar gwamnan Jigawa
  • AN YANKA TA TASHI: A biya ni naira miliyan 21 kuɗin fom ɗin takarar gwamna da na siya a PDP – Ɗan takarar gwamna

Abinda masu karatu ke fadi

  • Google on Masarautar Kano: Hassada Ta Sa Wasu Na Neman Wofintar Da Kokarin Su Danfodiyo! Daga Imam Murtadha Gusau
  • Kuşburnu Çekirdek Yağı on Dalilin da ya sa muka yi sallar Idi ranar Laraba a Bauchi, muka ki bin sanarwar Sarkin musulmi – Sheikh Dahiru Bauchi
  • Google on HARKALLAR BILIYAN 3.6: Ba nine Balan da ke jerin sunayen masu mallakin kamfanin Adda ba – Gwamna Bala
  • Google on SIYASAR ZAMFARA : Maitaimakawa tsohon dan takarar gwamna a APC akan harkar jarida ya sauya sheka
  • Google on RAMIN MUGUNTA: Yadda Boko Haram suka afkawa bam din da suka dana wa Sojojin Najeriya

Fanni

Tweets by PTimesHausa
  • All Homepage Blocks
  • Home
  • Home
  • Main Home

© 2022 JNews - Premium WordPress news & magazine theme by Jegtheme.

No Result
View All Result
  • Labarai
  • Labarai daga Jihohi
  • Wasanni
  • Kiwon Lafiya
  • Nishadi
  • Bidiyo da Hotuna

© 2022 JNews - Premium WordPress news & magazine theme by Jegtheme.