Hukumar NDLEA reshen jihar Jigawa ta kama muggan kwayoyimai nauyin kilogiram 50.5 da mutum 48 dake safarar su da tu’ammali da muggan kwayoyi a jihar.
Shugaban hukumar a jihar Maryam Gambo ta bayyana haka a garin dutse a makon jiya.
Maryam ta ce a iyakokin jihar da kasashen da ke makwabtaka da Najeriya ta kananan hukumomin Garki, Gumel, Babura, Maigatari da Sule Tankarkar ne aka kama wadannan mutane.
Maryam ta yi kira ga masu ruwa da tsaki da su hada hannu da gwamnati domin ganin an yaki muggan kwayoyi a jihar.
Idan ba a manta ba shugaban hukumar NDLEA Buba Marwa ya bayyana cewa nan ba da dadewa ba Najeriya za ta kawo karshen matsalar safara da ta’ammali da muggan kwayoyi a kasar.
Marwa ya ce yana da tabbacin cewa Najeriya za ta rage wannan matsala ne idan hukumar NDLEA ta ci gaba da samun goyon baya daga wajen gwamnatin tarayya, masu ruwa da tsaki da kungiyoyin bada tallafi na kasashen waje.
Ya ce tu’ammali da safarar muggan kwayoyi a kasar nan na kama da annobar cutar Korona inda a dalilin haka ya zama dole a mike tsaye wajen ganin an toshe duk kafar da ake amfani da su wajen shigowa da shan muggan kwayoyi a Najeriya.
Marwa ya kara da cewa hukumar na shirin bude ofisoshi a kananan hukumomin kasar nan amma rashin isassun ma’aikata ya hana hakan faruwa.
Ya ce hukumar za ta bude ofisoshin ta a tashoshin motoci da jirgin ƙasa domin kama masu safara da masu ta’ammali da miyagun kwayoyi.