Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa nan gaba za ta kafa wata hukumar tsaron da za ta riƙa aikin tsaro da kula da kan iyakokin Najeriya da ke fama da ƙalubalen rashin tsaro.
Mashawarcin Shugaba Muhammadu Buhari kan Tsaro, Babagana Monguno ne ya bayyana haka a Paris, babban birnin ƙasar Paris a wurin Taron Zaman Lafiya da ke gudana.
Taron wanda kuma ya samu halartar wasu hamshaƙan attajirai daga Najeriya da Faransa, an shirya shi ne domin bijiro da hanyoyin bunƙasa tattalin arziki da cinikayya ga Najeriya.
Manjo Janar (mai ritaya) Monguno ya ce ya lura kan iyakokin Najeriya sun kasance wurin shigowa da muggan haramtattun kayayyaki da kuma hanyoyin karakainar baƙin-haure da sauran masu aikata muggan laifuka da suka haɗa har da safarar mutane.
“Kan iyakokin da ke Arewa tsakanin ta da Nijar da Gabas tsakanin Najeriya da Chadi da kuma Kamaru da ta Gudu tsakanin ƙasar da Zirin Ruwan Guinea da Tekun Atilantika, kai har da gefen Yamma tsakanin mu da Jamhuriyar Birnin.
“Sai dai kuma faɗin ƙasa da wawakeken ruwan da ke kan iyakokin mu sun sa an kasa kula da su yadda ya kamata.
“A kan haka ne Hukumar Hana Fasa Ƙwauri ta bijiro da tsarin E-,Customs, yayin da Hukumar Shige-da-fice ta fito da tsarin kula da kan iyakoki na game-gari.
An daɗe ana danganta matsalar fantsamar muggan makamai a hannun ‘yan bindiga a Arewa maso Yamma da rashin kariya ga kan iyakokin da ake shigo da makaman, musamman ta ɓangaren jamhuriyar Nijar.
Kuma za a ƙarfafa tsaron haɗa-ka tsakanin jami’an tsaron Najeriya, Nijar, Jamhuriyar Birnin, domin a daƙile safarar muggan makamai da sauran masu aikata muggan laifuka a cikin ƙasashen uku.
Ya ce wannan mataki da aka ɗauka ya taimaka ƙwarai wajen rage manyan laifukan da ke faruwa.
A kan iyakar Najeriya da Kamaru da Chadi kuwa, tuni ake ganin ta can ne Boko Haram ke ƙara samun muggan makamai waɗanda suka shafe shekaru 12 kenan su na fafatawa da sojojin Najeriya, Nijar, Kamaru da Chadi.
Monguno ya ce fashin da ake yi a cikin ruwa ya zama abin damuwa sosai a yankin Afrika ta Yamma da kuma nahiyar baki ɗaya.